fbpx
Friday, May 27
Shadow

Tag: Dr. Junaid Muhammad

Ya kamata a saki sojan da ya caccaki Buratai saboda Gaskiya ya fada, Buratai dan Kasuwane yanzu>>Dr. Junaid Muhammad

Ya kamata a saki sojan da ya caccaki Buratai saboda Gaskiya ya fada, Buratai dan Kasuwane yanzu>>Dr. Junaid Muhammad

Tsaro
Tsohon dan majalisa a jamhuria ta 2, Dr. Junaid Muhammad ya bayyana cewa ya kamata a saki Lance Corporal Martins da yayi bidiyo ya caccaki shugaban sojoji, Janar Buratai da sauran manyan jami'an tsaro.   Yace sojan Gaskiya ya fada kuma tsareshi da ake yi bai kamata ba. A wani bidiyo da muka kawo muku a baya, Lance Corporal Martins ya bayyana cewa Buhari,  Buratai da Monguno duk sun baiwa Arewa kunya ganin cewa daga yankin suka fito amma gashi duk da haka ana ta kashe mutane.   Yace zai kaisu kara kotun hukunta manyan Laifuka ta Duniya ICC, Saidai Rahotanni da suka bayyana daga baya sun ce an kama sojan.   Junaid yace Buratai kamar dan kasuwa ya koma a gidan soja kuma ya gaza a aikinshi na tsare Najeriya daga hare-hare inda yace idan ba'a saki wancan ...
In ba korar shuwagabannin tsaro shugaba Buhari yayi ba, ‘yan Najeriya ba zasu taba gamsuwa ba>>Dr. Junaid Muhammad

In ba korar shuwagabannin tsaro shugaba Buhari yayi ba, ‘yan Najeriya ba zasu taba gamsuwa ba>>Dr. Junaid Muhammad

Tsaro
Tsohon dan majalisar tarayya a jamhuriya ta 2, De. Junaid Muhamad ya bayyana cewa idan shugaban kasa,Muhammadu Buhari ba korar shuwagabannin tsaro yayi ba to 'yan Najeriya ba zasu taba gamsuwa ba.   Yayi maganane akan gargadin bayabayannan da shugaban kasar yawa manyan jami'an tsaron inda yace aikinsu bai gamsar dashi ba. Dr. Junaid ya ce shekarun wadannan shuwagabannin tsaro 5 fa kenan suna abu daya kuma ba tun yau 'yan Najeriya ke sukarsu akan rashin kawo karshen matsalar tsaron kasarnan ba.   Yace koda janar ne aka turashi koyon aiki ko yaki yayi shekaru 4 zuwa biyar bai yi nasara ba ai an canjashi. Yace ba canka janarorin kadai ya kamata a yi ba, ya kamata kuma a bincikesu dan gano ko an yi almundahana da kudin al'umma.