
Shugaba Buhari bashi da lafiya>>Dr. Junaidu Muhammad
Tsohon dan majalisa na jamhuriya ta 2, Dr. Junaid Muhammad ya bayyana cewa kamata yayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sauka daga mukaminsa dan shi kanshi bai iya kula da kansa ballantana miliyoyin 'yan Najeriya.
Ya bayyanawa Sahara Reporters a ganawar da suka yi dashi cewa shugaba Buhari bashi da cikakkiyar Lafiyar da zai iya kula da Al'amuran kasarnan. Ya zargi hadiman shugaban kasa dana kusa dashi da yin rufa-rufa akan Lafiyar shugaban kasar.
Yace bai kamata anawa 'yan Najeriya rufa-rufa akan shugaban kasar ba, idan bashi da lafiya, ya kamata a sanar da mutane.
Yace ya rage ga yan Najeriya, Musamman Matasa su tsaya su bar shugaban kasar ya ci gaba da Mulki a haka ko kuma su nemi ya sauka.
“Being the President of the country, he...