
SIYASA BADA GABA BA: Ganduje Ya Taya Kwankwaso Murnar Cika Shekaru 64
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 64 a duniya.
Wanan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a cikin Jaridar Daily Trust, inda Ganduje yake taya Kwankwaso murnar cika shekaru 64.
A wannan rana ce madugun Darikar Kwankwasiyya, yake cika shekaru 64 a duniya. Wanda aka fara gudanar da bikin jiya a garin Muntare dake Karamar hukumar Rano a jihar Kano.
Bikin zai cigaba a wannan rana tare da bude sabon gidan rediyo mai suna Nasara, duka na daga cikin bangaren bikin nasa na cika shekara 64 a duniya.
Duk da irin hamayyar siyasar dake tsakanin Kwankwaso da Ganduje hakan bai hana shi taya tsohon mai gidan nasa murna ba.