An yi jana'izar Diyar Ministan Sadarwa da tattalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami me suna A'isha a masallacin Annur dake Abuja.
Daya daga cikin wanda suka halarci sallar jana'izar shine ministan Wuta, Sale Mamman inda yayi fatan Allah ya jikanta ya kuma baiwa iyalai hakurin rashi.
"Idan za ku lissafa Ministoci 2 ko 3 wadanda suka jajirce wajan aiki tukuru a cikin wannan gwamnatin, to mai girma Ministan Sadarwa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami ne na farko da yafi kowa jajircewa wajan yin aikin da ya dace.
Ya dauki ma'aikatar dake bacci ya inganta ta zuwa ingattaciyar ma'aikatar karni na 21, cewar Gwamna Nasir El-rufa'i
Rahotanni dake fitowa daga ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin Zamani wadda ke karkashin Minista, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami na cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karawa ma'aikatar karfi sosai.
Shugaban kasar ya amince da mayar da hukumar kula da Rijistar 'yan kasa ta NIMC karkashin kulawar ma'aikatar Dr. Pantami. Hutudole ya fahimci hakan na zuwane saboda gamsuwa da irin nasarorin da minstan ya samu a cikin shekara 1 da yayi yana aiki.
Sanarwar hakan ta fitone daga kakakin maaikatar, Uwa Sulaiman kamar yanda Hutudole ya samo muku da NTA. Wasu daga cikin nasarorin da Ministan ya samu sune ayyukan sadarwar zamani 260 a fadin Najeriya, Tabbatar da an yiwa sim din waya Rijista da kuma rufe wadanda ba'a wa Rijista ba. Hutudole ya ruwaito muku cewa ya kuma taimakawa...
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani kuma shehin malamin addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, ya kamata idan mutum ya ga mace ta yi shigar da bata dace ba to ya kauda kansa.
Malamin ya bayyana hakane a ganawar da yayi da BBChausa inda yake magana akan matsalar fyade. Hutudole ya kawo muku cewa malamin yace abin tsoro yayin da Allah ya jarabci mutane da wata fitina da jarabawa so ake a koma ga Allah da neman gafara amma kuma sai aka koma ci gaba da saba masa.
Malam yace dan mace ta fito tsirara bai kamata mutum ya kura mata ido ba ko kuma ya mata fyade ba. Yace akwai hakkin hukuma akwai hakkin iyaye akwai hakkin su kansu masu kallo abinda ya kamata ace su yi.
Malam ya jawo hankalin cewa a daina nunawa wanda akawa fyaden kyama.
A jiyane Ministar sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Sheikh Dr. Isa Ali Pantami ya saka hotunan yanda yayi aikin ragon layyarsa da kansa a shafinshi na sada zumunta.
Hakan ba karamin daukar hankula yayi ba sosai inda da dama suka yaba masa da kuma nuna sha'awa akai.
Saidai wasu abubuwa sun dauki hankula bayan da hotunan suka bayyana.
Minista da da hannun Hagu yake amfani(Bahagumene)
Wasu sun lura cewa Dr. Pantami da hannun Hafu yake amfani wajan aiki, kamar yanda suka bayyana ra'ayinsu a kasan hotunan nashi.
Saidai wasu na da ra'ayin cewa yanayin daukar hotonne yasa aka ga haka:
https://twitter.com/Mall_bodex/status/1289221165332885504?s=19
Wata ta dauki Hankula bayan da tace taso ace itace ke aikin:
Wata da tace...
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Ali Pantami kenan a wadannan hotunan a ganawar da yayi da farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasa ta kafar sadarwar zamani.
Ana sa ran cewa kudin da jama’a suke kashewa wajen yin kira a wayar salula zai ragu da kashi 40% bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa za a ga ragi a kudin waya bayan sun kwadaito da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.
Dr. Isa Ibrahim Pantami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shawo kan kalubalen da ake samu na kudin jawo igiyoyin RoW, da kuma tsare kayan aiki.
Sheikh Pantami ya yi wannan jawabi ne a wajen bude bikin koyon aiki da hukumar NITDA ta shirya wanda za ayi tsawon mako guda ana yi a birnin tarayya Abuja.
Ministan kasar ya shaidawa jama’a cewa cigaban da su ka kawo wajen kayan aikin sadarwa ya sa kamfanoni sun samu damar rage 40.18% na jama’a, d...