
Hotuna da Bidiyo: Yanda dakin Ka’aba ya kasance babu kowa Sanadin Coronavirus ya dagawa musulmai hankali
Hotunan yanda dakin ka'aba babu mutane ya dagawa mutane da dama hankali. Kasar Saudiyya ta dakatar da ayyukan Umara sanadin Cutarnan me kisa ta Coronavirus da ta bulla a kasar.
https://twitter.com/wasim_dr/status/1235624047335047168?s=19
Hakan yasa jama'a suka kauracewa dakin Ka'aba da a koda yaushe yake fal da jama'a ana bautar Allah.
Bidiyo da hotuna sun yi ta yawo a shafukan sada zumunta inda mutane sukai ta jimamin lamarin.
https://twitter.com/wasim_dr/status/1234574946963206156?s=19
Da dama sun bayyana cewa basu taba ganin dakin Ka'aba babu mutane ba sai a wannan karin,hakanan dutsen safa da Marwa ma babu jama'a.
https://twitter.com/wasim_dr/status/1235624457722646528?s=19
Duba kasa dan ganin wasu daga cikin hotuna lamarin.
&...