Wata mata ta zargi wani sanatan kasar Amurka da taba mata jiki ba tareda izininta ba: Ya nemi afuwa: kuma ya bukaci a bincikeshi
Wannan hoton wani sanatan kasar Amerikane me suna Alfranken da wata tsohuwar abokiyar aikinshi me suna Tweeden ta zargeshi da taba mata jiki ba tare da izininta ba. lokacin yana dan wasan barkwanci a shekarar 2006. Lamarin ya farune lokacin da abokan aikin biyu tare da wasu ma'aikata suka tafi gabas ta tsakiya gurin sojojin kasar ta Amurka dan nishadantar dasu.
Bayan sun isa kasar ne sai aka sanar da Tweeden cewa itama tana cikin wadanda zasu yi wasan na barkwancin kuma ana bukatar ayi sumbata a cikin wasan, a ranar da zasu gabatar da wasanne sai Alfranken ya bukaci suyi gwajin yin sumbatar shida Tweeden amma taki yarda, bayan ta saki jikine sai Franken ta lallabo ya kamo ta ya sumbaceta da karfi har sai da ta tureshi kuma ta gargadi kada ya kara mata haka.
Alfranken ya amsa laifinsa...