
Najeriya na daukar mataki dan hana Ebola data bayyana a kasashe Makwabta shigowa kasar
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana saka ido a iyakokin Najeriya dan ganin cewa cutar Ebola data bayyana a kasashen, Guinea da Congo Dr bata shigo Najeriya ba.
Gwamnatin ta bakin Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ta bayyana cewa an baiwa iyakokin Najeriya ta bangaren Ruwa da kasa umarnin kasancewa cikin shiri da Asibitoci da sauransu.
Ya kuma bayyana cewa kasar na Shirin karbar Rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19.