fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Ebonyi

Ebonyi: An gurfanar da Wani Matashi A Gaban Kotu Bisa Zargin Yiwa Wata Mai  Shekaru 20 Fyade

Ebonyi: An gurfanar da Wani Matashi A Gaban Kotu Bisa Zargin Yiwa Wata Mai Shekaru 20 Fyade

Crime
A ranar Litinin ne Aka gurfanar da wani Matashi mai shekaru 28, Chibueze Godwin a gaban wata Babbar Kotun dake jihar Ebonyi kan zargin yi wa yarinya ’yar shekara 20 fyade. Godwin, wanda ake zargi da aikata laifin, sun kasance zaune gida daya tare da wadda ake zargi da  yiwa fyaden kamar yadda aka bayyanawa kotun a yayin sauraron karar. Sai dai Wanda ake kara, Godwin ya musanta zargin da ake masa na aikata laifin a lokacinda ake tuhumar tasa. Itama lauyan mai kara Misis Grace Chima ta bukaci kotu da ta hanzarta Nemawa wacca aka ci zarafi hakkin ta. Daga bisani bayan sauraran duka bangarori biyun Mai shari’a Vincent Nwanchor, wanda ke jagorantar karar, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga Maris. (NAN)  
Gwamnan Jihar Ebonyi ya sha Al’washin hukunta duk masu kokarin tada zaune tsaye a Jihar

Gwamnan Jihar Ebonyi ya sha Al’washin hukunta duk masu kokarin tada zaune tsaye a Jihar

Tsaro
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a ranar Lahadi ya shelanta yaki da kungiyoyin asiri da ke kai hare-hare a kan mazauna Abakaliki da sauran sassan jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu sakamakon rikicin kabilanci da ake zargin kungiyoyin da ke gaba da juna a jihar suke haddasa wa. Gwamnan ya yi wannan ikrarin  ne a yayin da ya kai ziyara wata  coci dake Abakalikia A jihar ta Ebonyi, inda ya godewa magoya bayan sa, dama wadanda basa tare dashi ta fuskar tafiyar siyasa a jihar.    
Sauya sheka zuwa APC: An bukaci ‘yan majalisar Ebonyi su tsige Gwamna Umahi

Sauya sheka zuwa APC: An bukaci ‘yan majalisar Ebonyi su tsige Gwamna Umahi

Siyasa
Kusan mako guda bayan ficewar Gwamna Dave Umahi daga jam'iyyar People’s Democratic Party zuwa All Progressives Congress (APC), kungiyar 'Yan asalin jihar Ebonyi da ke zaune a kasashen waje (AESID) ta bukaci Majalisar da ta fara shirin tsige shi.   Kungiyar ta ce akwai matukar karya kundin tsarin mulkin Najeriya da hukuncin kotun koli, wanda ke dagewa kan cewa wani gwamna ba zai iya sauya sheka zuwa wata jam'iyyar siyasa ba har sai idan akwai wata takaddama ta shugabancin cikin gida ko bangaranci.   Dan haka kungiyar a cikin wasikar da suka aikewq majalisar suka nemi a tsige gwamnan.   In view of the foregoing breaches of the fundamental rights of citizens of our dear State, therefore, and the potentialities of same to plunge Ebonyi into a serious politi...
Ba zamu bi Gwamna Umahi zuwa APC ba>>’Yan Majalisar Jihar Ebonyi

Ba zamu bi Gwamna Umahi zuwa APC ba>>’Yan Majalisar Jihar Ebonyi

Uncategorized
'Yan Majalisar Jihar Ebonyi sun bayyana cewa ba zasu bi gwamnan jihar,  Dave Umahi zuwa Jam'iyyar APC ba.   Sun bayyana hakane a sanarwar da suka fitar jiya a Abuja wajan taro na musamman da suka yi. Shugaban 'yan majalisar da suka fito daga jihar, Sanata Sam Egwu ya bayyana cewa, da sanatoci da 'yan majalisar wakilai na jihar ba zasu koma jam'iyyar APC ba.   Yace tabbas suna da ra'ayin cewa kowace jam'iyya a 2023 ta tsayar da dan takarar shugaban kasa daga yankinsu amma wannan ba dalili bane da zai sa su juyawa jam'iyyar su baya ba. Yace gwamnan shine kusan ya fi kowa morat jam'iyyar ta PDP da kuma bai kamata ya juya mata baya ba.
Ina Alfahari da kai sosai>>Shugaba Buhari ya gayawa Gwamna Dave Umahi bayan da ya koma APC

Ina Alfahari da kai sosai>>Shugaba Buhari ya gayawa Gwamna Dave Umahi bayan da ya koma APC

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyanawa Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi cewa yana Alfahari dashi bisa komawa APC da yayi daga PDP.   Hakan na kunshene cikin wata Sanarwa da shugaban kasar ya fitar ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu inda yace Gwamna Umahi ya koma APC ne saboda nagarta, ba tursasashi aka yi ba.   Yace yayi farin ciki da gwamnan ya hangi nagartar APC ya koma cikinta sannan kuma da irin Gwamna Umahi a APC za'a samu nasara sosai a karfafa Dimokradiyya. Shehu quoted Buhari as saying that, “I am proud of Governor David Umahi, for taking this bold decision in accordance with his conscience and principles rather than any external influence or coercion. “Good governance is very important to us in the APC, and I am glad that the governor has ci...
Gwamna Umahi: Dalilin da ya sa na bar PDP

Gwamna Umahi: Dalilin da ya sa na bar PDP

Siyasa
Gwamnan Umahi, wanda ya tabbatar da cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party zuwa All Progressive Congress, ya ce ba zai yi nadamar wannan shawarar ba ko ko kadan. “Yace dole ne in jagoranci zanga-zangar adawa da nuna wariyar launin fata da ake yi wa‘ yan kabilar Ibo da PDP ta yi, kuma ba sai na tuntubi kowa ba don ya jagoranci irin wannan zanga-zangar. “Ba na son PDP ta fadi a yankin Kudu maso Gabas amma tana iya durkusar da kanta a shiyyar idan ba ta bi shawarar mutanen ba don shigar da adalci, gaskiya, da daidaito.
Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze ta goyi bayan gwamnan Ebonyi ya koma APC

Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze ta goyi bayan gwamnan Ebonyi ya koma APC

Siyasa
Kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze ta bayyana goyon bayanta ga gwamnan jihar Ebonyi,  Dave Umahi ya koma jam'iyyar APC.   Rahotanni sun bayyana cewa saboda kin amincewar PDP ta baiwa yankin Inyamuran takarar shugaban kasa a shekarar 2023, gwamnan yace zai koma APC.   Sakataren kungiyar, Chucks Ibegbu be ya bayyanawa Punch cewa suna tare da Umahi saboda PDP bata musu Adalci.   Saidai APC tace har yanzu Umahi be sanar da ita a hukumance cewa zai koma jam'iyyar ba amma dai kofarta a Bude take ga kowa.
Bata gari sun kashe dansanda sannan suka yanke mai mazakuta Ebonyi

Bata gari sun kashe dansanda sannan suka yanke mai mazakuta Ebonyi

Siyasa
Rahotanni daga jihar Ebonyi na cewa wasu bata gari sun kaiwa wani ofishin 'yansanda sake Abakaliki hari.   Matasan dauke da makamai sun kona ofishin 'yansandan da ababen hawa da dama sannan suka kashe wani dansanda suka kuma yanke masa mazakuta da dauke bindigar sa.   Kakakin 'yansandan jihar, Loveth Odah ce ta tabbatar da hakan inda tace bata garin sun yi banna sosai a jihar.
Kunwa Kanku: Bazan gyara Gine-ginen Gwamnati da aka lalata ba da sunan zanga-zangar SARS>>Gwamnan Ebonyi

Kunwa Kanku: Bazan gyara Gine-ginen Gwamnati da aka lalata ba da sunan zanga-zangar SARS>>Gwamnan Ebonyi

Siyasa
Gaamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya bayyanawa mutanen jiharsa cewa duk wani ginin gwamnati da shine ya ginashi kuma aka lalata da sunan zanga-zangar SARS to ba zai sake ginashi ba.   Gwamnan ya bayyana hakans yayin da yake zagaye dan ganin irin barnar da aka yi da sunan zanga-zangar SARS.   Yace an kona ofisoshin 'yansanda 4 inda yace 2 daga ciki shine ya ginasu dan haka ba zai sake ginawa ba, yace 2 kuma na hayane ake amfani dasu dan haka zai yi kokarin ganin an sake ginasu.   Gwamnan yace mutane ya kamata su tashi su kare duk wani ginin gwamnati dake yankinsu saboda dan su aka yi shi.   Gwamnan yace wanda kuma suka jikkata gwamnati zata taimaka a basu kulawa muddin dai basa cikin masu tada zaune tsaye.   “My position is that any faci...
Yansanda na binciken kisan da akawa Fulani 2 a jihar Ebonyi

Yansanda na binciken kisan da akawa Fulani 2 a jihar Ebonyi

Siyasa
Yansanda a jihar Ebonyi sun yi Allah wadai da kisan da akawa wasu matasan Fulani 2 a Dajin Ishieke dake karamar hukumar Ebonyi a jihar.   Wanda aka kashe din sune Adamu Ibrahim dan Shekaru 7 da Jubril Ibrahim da shekaru 15, Rahoton 'yansanda da kakakin 'yansandan jihar, Loveth Odah ta fitar ya bayyana cewa an kaiwa fulanin hari rugarsu ne inda aka kashe yaran 2. Hukumar 'yansandan tace ta fara binciken lamarin inda kuma ta jawo hankalin mutane da kada a ce za'a je harin daukar fansa a kwantar da hankula.