
Atiku Abubakar yaui Alhinin rasuwar mutane a Gobaraf tankar Kogi
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi jimamin rasuwar mutane da yawa a jihar Kogi biyo bayan gobarar Tankar Mai.
Lamarin ya farune a Felele kan hanyar Lokoja zuwa Abuja.
A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumuntar Twitter, Atiku yace ya damu da gobarar tabkar mai data faru a Lokoja da Hadarin da ya faru a jihar Ebonyi wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama. Yayi musu fatan Samun Rahama.
https://twitter.com/atiku/status/1309164120982392834?s=19
Yace a madadinsa da iyalansa yana mika sakon ta'aziyya ga jama'ar Jihar Kogi da Ebonyi.