
Shugaba Buhari ya amince da baiwa ECOWAS tallafin Dala Miliyan 20 dan yakar ta’addanci
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da baiwa ECOWAS tallafin dala Miliyan 20 dan yakar ta'addanci.
Wannan alkawali ne wanda gwamnatin Najeriya ta yi a baya wanda shugaban kasar kuma ya cikashi. Sannan a Najeriya ma, Shugaban kasar ya amince da fitar da dala Miliyan 80 dan yakar ta'addanci a Arewa maso yamma da Arewa maso Gabas.
Shugaban ya bayyana hakane da kansa a wani jawabi da yayi wajan taron kungiyar ta ECOWAS inda kuma ya bada shawarar cewa a rage yawan ma'aikatam kungiyar.
”We have already directed the immediate remittance of the sum of $20 million pledged by Nigeria to the pool account of the ECOWAS Action Plan to fight terrorism, while the sum of $80 million is to be disbursed for the fight against terrorism in the Northeast and banditry in t...