fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Edinson cavani

Cavani na shirin barin Manchester United

Cavani na shirin barin Manchester United

Wasanni
Edinson Cavani yayi burus da tayin sabunta zaman shi a kungiyar Manchester United, bayan da dan wasan ya mayar da hankulan shi wa komawa arewacin kasar Amurka da taka leda.   Cavani ya koma United ne da kwantirakin shekara guda a kakar bara bayan ya bar kungiyar PSG,yayin daya yi nasarar ciwa Manchester United kwallaye bakwai a cikin wasanni 25 wanna kakar.   Manema labarai na kasar Argentina me suka ruwaito wannan labarin cewa Cavani nada ra'ayin komawa Boca Juniors domin yayi ritaya a kungiyar, domin hakan ya kasance babban burin shi.   Edinson Cavani 'rejects' Man Utd contract extension Edinson Cavani has reportedly turned down the offer of a Manchester United contract extension in order to return to South America.   The veteran forward joined ...
‘Yan wasan gaba na Manchester United basu kai kwarewar Cavani ba>>Pogba

‘Yan wasan gaba na Manchester United basu kai kwarewar Cavani ba>>Pogba

Uncategorized
Mashahurin dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa dake taka leda a kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa yan wasan gaba na tawagar United basu kai matakin Edinson Cavani ba. Pogba ya fadi wannan maganar ne bayan da shi da Cavani suka yi nasarar ciwa Manchester kwallaye biyu a wasan data doke Fulham daci 2-1 a daren jiya, inda ta dare saman teburin gasar Premier League. Ana sa ran cewa Edinson Cavani zai dan ringa taimakawa ne kawai ga yan wasan gaba na United masu karancin shekaru, amma sai dai dan wasan ya jajirce sosai inda ya bayyana cewa shima fa yana daga cikin manyan yan wasa a kungiyar. Manchestee United Strikers are not at the same level as Edinson Cavani>>Pogba Paul Pogba has claimed Man Utd's strikers do not possess the same quality as veteran ...
Manchester United na harin sabuntawa Edinson Cavani kwantiraki

Manchester United na harin sabuntawa Edinson Cavani kwantiraki

Wasanni
Manajan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya bayyana cewa tauraron dan wasan shi Edinson Cavani zai taka muhimmyar rawa a kungiyar yayin da kuma ya kara da cewa dan wasan zai iya sabunta kwantirakin shi a kungiyar. Edinson Cavani ya koma kungiyar Manchester United ne daga Paris Saint German a kyauta da kwantirakin shekara daya tare da zabin karin watanni 12, bayan ya bar kungiyar PSG wadda ya dauki tsawon shekaru 7 yana buga mata wasa. Wasa daya kacal Cavani ya fara bugawa Manchester daga farko, yayin da kuma yayi nasarar cin kwallaye 3 a wasanni takwas daya buga mata amma saidai yawancin wasannin nashi daga benci yake shigowa yayin da har ya taimakawa Fernandez yaci kwallo guda a wasan su da Leicester City.
Southampton 2-3 Manchester United: Yayin da Edinson Cavani ya zamo dan wasa na biyu daya taimakawa United da kwallaye uku bayan shiga wasa daga benci tun bayan Ole Gunnar

Southampton 2-3 Manchester United: Yayin da Edinson Cavani ya zamo dan wasa na biyu daya taimakawa United da kwallaye uku bayan shiga wasa daga benci tun bayan Ole Gunnar

Wasanni
Yan wasan takwas ne kadai suka fi Ward Prowse cin kwallaye nesa wato free kick a gasar Premier league, yayin kwallon daya ciwa Southampton bayan Bednarek ya ci tashi kwallon ta zamo tara kuma yayi daidai da Redknapp, Nolberto da kuma Frank Lampard. Bruno Fernandez ne ya fara ramawa United kwallo guda a wasan da taimakon Cavani wadda tasa ya zamo dan wasa na hudu da yayi nasarar ciwa Manchester kwallo a wasanni biyar wanda bana gida ba a jere. Sai Edinson Cavani yayi nasarar cin kwallaye biyu yayin da shi kuma ya zamo dan wasa na biyu daya  taimakawa Manchester United da kwallaye uku a wasa guda daga benci, tun bayan manajan kungiyar na yanzu Ole Gunnar wanda shi yaci kwallaye hudu daga benci a wasan su da Nottingham.
Manchester United 0-0 Chelsea: Yayin da Edinson Cavani ya fara buga wasan shi na farko a kungiyar Manchester

Manchester United 0-0 Chelsea: Yayin da Edinson Cavani ya fara buga wasan shi na farko a kungiyar Manchester

Wasanni
Sabon dan wasan Manchester United wanda ta siya a ranar da aka kulle kasuwar yan wasa, Edinson Cavani ya fara bugawa kungiyar wasa a yau bayan tayi mai mai canji a minti na 58 a wasan da suka tashi 0-0 tsakanin su da Chelsea a gasar Premier league. Manchester United ta cigaba da rashin nasara a wasannin ta na gida har guda uku data fara bugawa na wannan kakar wanda hakan ya kasance karo na farko tun kakar 1972/73. Kocin Chelsea Lampard ya yabi golan shi Mendy bayan an tashi saboda kwallayen daya yi nasarar cirewa a wasan. Kiris ya rage kungiyar Chelsea ta samu penariti bayan Harry Maguire ya bugi Azplicueta amma alkalin wasan bai bayar da penaritin ba wanda hakan yasa kaftin din Chelsea ya kalubalanci na'urara VAR a bayanan daya yi bayan an tashi wasan.
Na kusa yin ritaya bayan cutar korona ta kama budurwa ta>>Edinson Cavani

Na kusa yin ritaya bayan cutar korona ta kama budurwa ta>>Edinson Cavani

Wasanni
Edinson Cavani ya koma kungiyar Manchester United ranar litinin a kyauta da kwantirakin shekara daya tare da zabin kara wata shekara a kungiyar Premier League din, wadda ya bayyana cewa ta kasance daya daga cikin mayan kungiyoyin duniyar wasan kwallon kafa. Dan wasan mai shekaru 33 zai samu albashin yuro miliyan 11 a kowace shekara daga United tare da karin yuro miliyan 2 sai kuma karin wasu yuro miliyan 4 na siyen shi da suka yi. Cavani ya kasance tsohon dan wasan PSG wadda ya bari a karshen kakar data gabata bayan dauki tsawon shekaru 7 a kungiyar. Kuma dan wasan ya samu kwantiraki daga wasu kungiyoyi amma ya fara tunanin yin ritaya saboda annobar korona ta fara shafar iyalan shi. Cavani ya bayyana cewa "A koda yaushe lafiyar iyalai ce a sahun farko, mun sha fama da cutar korona ta...
Edinson Cavani ya amince da kwantirakin shekaru biyu daga kungiyar Manchester United

Edinson Cavani ya amince da kwantirakin shekaru biyu daga kungiyar Manchester United

Wasanni
Edinson Cavani yana shirin zama sabon dan wasan Manchester United na biyu a wannan kakar yayin da kuma zai ringa fuskantar takara daga wurin Anthony Martial a kungiyar, bayan United ta amince zata biya shi yuro miliyan 20. Manchester United ta fara tattaunawa da tsohon dan wasan PSG da Napolin ne a cikin wannan makon bayan sun yanke shawarar cewa farashin  da Dortmund ta sawa Jadon Sancho na yuro miliyan 107 yayi yawa. A ranar sati jigajigan kungiyar Manchester United suka tabbatar da cewa yarjejeniyar su da Cavani tayi armashi kuma yanzu dan wasan zai saka hannu a takaddun kwantirakin shekaru biyu a United din.