
‘Yan sanda A jihar Ondo Sunyi Nasarar cafke wani sojan bogi
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo ta cafke wani sojan bogi dan shekara 24 mai suna Desmond Ikechukwu.
An kama wanda ake zargin ne sanye da kakin Sojoji.
Binciken da Daily Sun ta yi ya nuna cewa an kama sojan gonan ne a yankin Araromi da ke Akure, babban birnin jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Bolaji Salami ya ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya kasance yana amfani da kakin sojoji na bogi don tsoratar da jama’a kuma tuni da aka tuhume shi akan laifin nasa ya amsa cewa ya aikata.
Haka kuma Kwamishinan ya ce an kama wasu mutane 20 da ake zargi da satar mutane, fashi da makami da kuma lalata da kananan yara.
A karshe kwamishina ya bayyana cewa za'a gurfanar da masu laifin a gaban kuliya da zarar rundunar ta kammala binci...