
Yawan mutanen da ake kashewa yanzu sun fi wanda aka kashe a yakin Basasa>>Edwin Clark
Dan siyasa kuma tsohon Ministan Labarai daga kudancin Najeriya, Edwin Clark ya bayyana cewa yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu ya fi wanda aka kashe a lokacin yakin Basasa.
Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi da Sunnews. Yace babu Dimokradiyya a Najeriya domin mulkin da ake yi a yanzu yama fi na Soja Muni.
Ya kara da cewa dan hakane ma suka kai gwamnati kara inda suke neman a biyasu Biliyan 50 a matsayin diyyar na daidai ba da aka aikata musu.
Da yake magana akan matsalar tsaro yace abubuwa kullun sai kara tabarbarewa suke, uace yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya a yanzu yafi wanda aka kashe a lokacin yakin basasa.
Yace ka duba kasar Amurka, mutum 1 ne aka kashe amma gaba daya hankula sun tashi amma a Najeriya sai a k...