
Daya daga cikin manyan jami’an gwamnatin shugaba Buhari yayi barazanar yin Murabus
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa yayi barazanar cewa zai iya ajiye aikinsa idan aka tursasashi sai yayi abinda ya sabawa doka.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na kasa, watau, NTA.
Yace a Najeriya kawai mutane da sunga me kudi sai su yi ta binsa, ba'a tunanin ina ya samo kudin, yace suna kokarin hada kai da shuwagabannin al'umma dana addinai wajan yaki da rashawa da cin hanci.
Ya bayar da tabbacin cewa, EFCC a karkashinsa zata zama me aiki da doka da oda kuma idan aka yi yunkurin tursasashi ya yi abinda bai dace ba to zai ajiye mukaminsa ne kawai.
A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda EFCC ta kama wasu 'yan damfara
“We need to change our attitudes in Nigeria,” Bawa was quoted to ...