
Kasar Egypt ta hako makara 13 da aka binne shekaru sama da Dubu 2 ba tare da sun lalace ba
Kasar Egypt ta bayyana gano wasu makara 13 da aka binne shekaru 2,500 da suka gabata wanda kuma babu abinda ya samesu.
Ma'aikatar kula da kayan Tarihi ta kasar ta bayyana cewa an gano makaranne a yankin Saqqara dake Giza na kasar.
Ministan ma'aikatar , Khaled Al-Anany da sakataren ta, Mostafa Waziri sun kai ziyara wajan inda suka shaidawa Xinhua cewa wannan ne katin farko da aka gano makara da yawa a kasa tun bayan wanda aka gano guda 30 a shekarar 2019.
Yace har yanzu dai basu kammala tantance makara nawa aka gano ba amma zasu ci gaba da aikin Hakowa.