fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Eid

Mai Al’farma sarkin Musulmi  ya yi kira da Musulmai su gudanar da Sallolin Eid a masallatan Juma’a

Mai Al’farma sarkin Musulmi ya yi kira da Musulmai su gudanar da Sallolin Eid a masallatan Juma’a

Kiwon Lafiya
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Juma’a 31 ga watan Yuli a matsayin ranar Sallar Eid-el-Kabir tare da yin kira ga Musulmi da su gudanar da salla a masallatai. Alhaji Sa'ad Abubakar shine  shugaban majalisar koli na addinin musulunci na kasa (NSCIA) ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini Farfesa Sambo Junaidu, ya gabatar wa manema labarai ranar Alhamis a Sakkwato. Bayanin ya kara da cewa: "Saboda halin da ake ciki a yanzu sakamakon cutar COVID-19, Sarkin Musulmi ya ba da shawara ga Shugabannin Gundumomi da na limamai da ke jihar Sakkwato, da su yi sallar Eid a masallatan Juma'at din su.