
Yan bindiga sun kashe wani fasto‘ yayin da yake kokarin girbar ayaba a jihar Ekiti
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani fasto, Mista Kayode Ogunleye, inda suka jefa gawarsa a wani daji a kan babbar hanyar Aramoko-Ijero-Ekiti a Ekiti.
An gano gawar faston, wanda shi ma ma’aikaci ne na Karamar Hukumar Ekiti ta Yamma, a gonarsa da ke kusa da dajin.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kashe Ogunleye, wanda ke aiki a cocin All Christian Fellowship Church yayin da yake aiki a gonarsa.
An ce an harbe shi ne yayin da yake kokarin girbin ayaba a gonarsa.
Daya daga cikin majiyoyin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana kisan na Ogunleye a matsayin na dabbanci, yana kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka yi kisan.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda a Ekiti, Mista Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin da ak...