
Elclasico:Real Madrid ta lallasa Barcelona 3-1
A wasan Elclasico da aka buga tsakanin Real Madrid da Barcelona a yammacin yau, Asabar, Real Madrid din ta lallasa Barca da 3-1.
Valverde ne ya fara ciwa Real Madrid kwallo inda Ansu Fati ya farke ta, kuma hakan shine ya bashi damar zama dan wasa mafi karancin shekaru da yaci kwallo a Elclasico a karni na 21.
Ramos da Modric sun ci kwallaye dai dai wanda a haka aka tashi wasan. Da wannan nasa, Real Madrid ta yi nasara sau 97 yayin da Barcelona ta yi sau 96 a wasannin Elclasico da suka buga.
Wasanni 6 kenan Messi na bugawa da Real Madrid ba tare da ya ci ko daya ba.