
Kotu ta bukaci sanata Elisha Abbo ya biya matarnan da yaci zarafinta a shagon sayar da kayan jima’i diyyar Miliyan 50
Rahotanni daga Abuja na cewa, Babbar Kotun tarayya ta yanke hukuncin bukatar Sanata Elisha Abbo ya biya matarnan da ya ci zarafinta a shagon siyayyar kayan jima'i na roba diyyar Miliyan 50.
A hukuncin da kotunnta yanke yau, Litinin, ta bukaci sanata Elisha Abbo ya biya Osimibibra Warmate diyyar Miliyan 50.
A watan Maris na shekarar 2019 ne dai Aka zargi sanatan da cin zarafin matar wanda kuma makwanni da suka gabata, Alkalin kotun Magistre ya wankeshi.