fbpx
Monday, May 23
Shadow

Tag: Elrufai

Nasha wahala lokacin da nake jinyar Cutar Coronavirus – A cewar Nasir Elrufai

Nasha wahala lokacin da nake jinyar Cutar Coronavirus – A cewar Nasir Elrufai

Kiwon Lafiya
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a karo na farko ya bayyana halin da ya tsinci kansa yayin da yake jinyar cutar coronavirus a cibiyar killace wadanda suka kamu. El-Rufai, wanda aka gano yana dauke da cutar a ranar 28 ga watan Maris, ya zama mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da ita a jihar ta Kaduna – inda aka killace shi na tsawon kwana 26 kafin daga bisani ya murmure aka kuma sallame shi daga cibi yar – bayan an yi masa gwajin da ya nuna ya warke. Gwamnan, wanda ya yi wata ganawa ta kai-tsaye cikin harshen Hausa da wasu zababbun gidajen rediyo a Kaduna ranar Talata da maraice, ya ce ya sha fama da ciwon kai mai tsanani tare da zazzabi a makon farko bayan killace shi. Sai dai ya ce bai san takamaimai ko a ina ko kuma ranar da ya harbu da cutar ta coronavirus ba,...