
Da Duminsa: Shugaban Faransa ya warke daga Coronavirus/COVID-19
Rahotanni daga kasar Faransa na cewa shugaban kasar, Emmanuel Macron ya warke dsga cutar Coronavirus/COVID-19 da ta kamashi.
Sanarwar ta fito ne daga fadar shugaban kasar Faransa inda tace sau 2 ana gwada Shugaba Macron kuma sakamakon na nuna cewa bashi dauke da cutar.
Dan haka sanarwar tace shugaban zai fito daka killacewar da yawa kansa.