
Shugaban ‘yansandan Najeriya ya fara binciken neman dakatarda bin ba’asin cin zalin ‘yansanda
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu ya fara binciken masu kula da Shari'a na hukumar kan neman kotu ta dakatar da bin ba'asin da ake na cin zalin Rundunar SARS da aka rusa.
Kakakin hukumar 'yansandan, Frank Mba ya bayyana cewa, an tuhumi me kula da bangaren shari'a na hukumar 'yansandan kuma idan an sameshi da laifi za'a hukuntashi.
Yace shugaban 'yansandan na aiki Tukuru wajan ganin an tabbatar da rusa rundunar ta SARS.