
Wani mummunan Hadarin Mota yayi sanadin salwantar rayukan mutum 3 tare da jikkata wasu da dama a jihar Enugu
Akalla mutane uku ne suka mutu a ranar Alhamis a wani hatsarin mota da ya fari a kan hanyar Abaomege-Afikpo dake karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Abakiliki dake babban birnin jihar.
A cewarsa, mutane hudu sun samu munanan raunuka a hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 2 na dare.
Wani shaidar gani da ido, Mista Joseph Okoro, ya shaida cewa lamarin ya faru ne sakamakon fashewar ta yar motar a lokacin da motar ke gudu kan titi.
An dai garzaya da wadanda suka samu rauni izuwa Asbiti mafi kusa inji shi.