
Farashin Manja yayi Gwauran zabi A wasu sassan kusawanni
Rahotanni na nuni da cewa, an samu hauhawar farashin Manja a wasu manyan kasuwanni dake ciki da wajan jihar Enugu da ke kudancin Najeriya kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito.
A rahotan da Kamfanin Dillancin labaran ya gabatar ya bayyana cewa, Farashin Manjan ya karu da kusan kaso 25, idan a ka kwatanta shi da kwanakin baya.
Farsahin manjan a wasu kasuwanin jihar da su ka hada da, Akwata Garki, da Mayor ya kai 5,000 a kan kowanne galan wanda ada ake sayar dashi a kan farashin Naira 2,900.
Hakanan kowacce kwallaba ake sayar da ita akan Naira 700 mai makon 500, yayin da ko wacce jarka ake sayar da ita akan farashin Naira Dubu 25 ko 24.