Gwamnatin tarayya ta sanar da kammala gyaran filin jirgin saman Akanu Ibiam dake jihar Enugu.
Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya bayyana haka bayan ziyarar gani da ido da yaje filin jirgin saman.
Yace a yanzu fimin jirgin saman ya kammalu kuma nan bada jimawa ba za'a kaddamar dashi.
An rushe ginin wani mutum da a ka bayyana da suna John Jerry bayan ya jagoranci wasu gungun 'yan daba, inda suka rushe shingen filin jirgin sama na jihar Egunu, yayin da yayi ikrarin cewa filinsa ne.
Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika shine ya bayyana cewa, Jami'an 'yan sanda sunyi nasarar cafke Mutumin wanda ya jagoranci tawagar daruruwan 'yan daba suka rushe katangar Filinjirgin sama har tsawan mita 2Km.
A yayin ziyarar gun da lamarin ya faru ministan ya nuna rashin jin dadin sa tare da Nuna takaicin sa, game da matakin da mutumin ya dauka na rushe shingen filin jirgin.
Daga bisani shima mutumin an rushe gidan sa, dake kan titin Eziokwe, gaza da Awowi 24 bayan rushe shingen filin jirgin saman da yayi.
Shima A ta bakin shugaban hukumar (ECTDA) na jihar Enugu Josef ...
Wani Magidanci Dan kasar Ghana dake zaune a jihar Enugu shida iyalinsa, ya shiga hannun hukuma bayan da ya zubawa matarsa tafa shashshan ruwan safi a kan Kirjinta.
Mutumin mai suna Emmanuel Opoku, an rawaito cewa Jami'an tsaro sun yi nasar cafke shi bayan da a ka zarge shi da zubawa matarsa ruwan zafi a lokacin da take shayar da yaron su da bai wuce wata uku da haihuwa ba.
Lamarin ya faru ne bayan da matar ta tambayi mijin nata kudin sayan kayan abinci, lamarin da ya fusata magidancin har ta kai ga ya kwarara mata ruwan zafi a kan kirji.
Wata kungiya mai zaman kanta ta mata, wadda a turance a ke kira da WomenAids Collective WACOL, ita ce ta Sanar da labarin ta kafafan sadarwa.
Kungiyar ta bayyana cewa a ranar 9 ga watan Yuli ta samu labari inda wani magidanci ya zubawa matars...