
Dadumiduminsa: Manchester City ta tanadi yuro miliyan 100 don sayen Haaland a karshen wannan kakar
Manchester City ta shiryawa sayen tauraron dan wasan Dortmond, Erling Haaland dan shekara 21 wanda ya kasance daya cikin kwararrun yan wasan gaba na duniya.
Haaland ya ciwa Dortmund kwallaye 16 a wasanni 14 wannan kakar, kuma Manchester City ta tattauna da dan wasan akan sayen sa yayin da ta tanada yuro miliyan 100 don sayensa a karshen wannan kakar.
Barelona, PSG da Real Madrid duk suna harin sayen dan wasan amma da yuiyuwar City zai zaba. Kuma kamar yadda Dortmund ta fada a baya sai karshen wannan kakar ne zata sa mai farashin yuro miliyan 63.