fbpx
Saturday, November 28
Shadow

Tag: Everton

Fulham 2-3 Everton: yayin da Calvert Lewin ya taimakawa Everton da kwallaye biyu ita kuma Fulham ta cigaba da barar da penariti

Fulham 2-3 Everton: yayin da Calvert Lewin ya taimakawa Everton da kwallaye biyu ita kuma Fulham ta cigaba da barar da penariti

Wasanni
Tauraron dan wasan Everton Richarlison ya cigaba da jajircewa bayan daya kammala dakatar da shi daga wasanni uku da aka yi, yayin daya taimakawa Calvert Lewin yayi nasarar ciwa Everton kwallo guda cikin minti daya da fara wasan nasu. Decordova ya ramawa Fulham kwallon da Lewin ya zira masu a minti na 15 yayin da shi kuma dan wasan Ingilan Calvert ya kara zira wata kwallon da taimakon Digne wadda tasa ya kasance dan wasan daya fi zira kwallaye a gasar Premier League wannan na kakar da kwallaye 10. Dan wasan baya na faransa Digne ya kara taimakawa Doucoure ya ciwa Everton kwallon ta uku a wasan wadda tasa kungiyar ta lashe gabadaya maki uku na wasan duk da cewa Fulham ta kara zira kwallo guda ta hannun Lucas Loftus. Sakamakon wasa yasa yanzu Fulham ta fadi wasanni bakwai...
Everton 1-3 Manchester United: Yayin da Cavani yaci kwallon shi ta farko kuma Fernandez ya taimakawa Ole Gunnar da kwallye biyu

Everton 1-3 Manchester United: Yayin da Cavani yaci kwallon shi ta farko kuma Fernandez ya taimakawa Ole Gunnar da kwallye biyu

Wasanni
Manchester United tazo daga baya tayi nasarar lallasa kungiyar Everton 3-1 a wasan da Ole Gunnar yake bukatar samun nasara bayan ya fadi wasanni biyu a jere tsakanin shi da Arsenal da kuma Instanbul Baskasehir. Manajan Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer har ya fara firgita bayan Bernard yasa tawagar Carlo Ancelotti ta fara jagorantar wasan. Amma daga bisani tauraron dan wasan shi na kasr Portugal, Bruno Fernandez ya kwantar mai da hankali tun kafin aje hutun rabin lokaci bayan da yayi nasarar cin kwallaye guda biyu. Yayin da shima sabon dan wasan Manchester Cavani yayi nasarar cin kwallon ta farko a kungiyar wadda ta tabbatar da cewa Ole Gunnar ya lashe gabadaya maki uku na wasan. Bruno Fernandes rescued Man united from falling to another defeat after netting a...
Premier League: Everton ta rike Liverpool 2-2

Premier League: Everton ta rike Liverpool 2-2

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta rike Liverpool 2-2 a wasan da suka buga yau na gasar Premier League.   Sadio Mane ne ya fara ciwa Everton Kwallo ana mintuna 3 kacal da take wasa saidai Michael Keane ya farkewa Everton kwallon a mintuna 19. Mohamed Salah ya ci kwallo ta 2 ana mintuna 72 da wasa sai dai Dominic ya farke ta a mintuna 82, Everton ta kare wasan da 'yan wasa 10 saboda an baiwa Richarlison jan kati.   Henderson ya ciwa Liverpool kwallo a kurarren lokaci amma an hanata.   An yi karan batta tsakanin Virgil Van Dijk da golan Everton, Jordan Pickford wanda yar hakan tasa aka fitar da Van Dijk waje.
Everton 5-2 West Brom: Yayin da James Rodriguez yaci kwallon ta farko a Eveton shi kuma Calvert yaci Hat Trick

Everton 5-2 West Brom: Yayin da James Rodriguez yaci kwallon ta farko a Eveton shi kuma Calvert yaci Hat Trick

Wasanni
A yau kungiyar Everton ta karbi bakuncin West Brum yayin da suka lallasa bakin nasu bayan Calvert Lewin yayi nasarar cin Hat Triick karo na farko wanda hakan ya taimakawa kungiyar tashi tayi nasarar cin 5-2 tsakanin su da yan wasa goma bayan an ba Kieran Gibbs jan kati kuma har alkalin wasan ya korin kocin West Brom Slaven Bilic. Calvert Lewin ya taka muhimmiyar rawa sosai a wasan yayin da shima tsohon dan wasan Real Madrid James Rodrigues ya ci kwallon shi ta farko a Everton kuma ya kasance a cikin rikicin daya sa aka baiwa Kieran Gibbs jan kati. Everton yanzu tayi nasara a gabaya wasannin ta uku data buga yayin ita sabuwar kungiyar Premier League West Brom take neman maki na farko a gasar. West Brom ne suka fara jagorantar wasan bayan Grady Diangana ya ci masu kwallo guda kafin...