fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: FA Cup

Hotuna: Kalli yanda Arsenal ta yi murnar lashe kofin FA karo na 14

Hotuna: Kalli yanda Arsenal ta yi murnar lashe kofin FA karo na 14

Wasanni
A yaune Arsenal ta zo daga baya, bayan Chelsea ta mata 1-0 ta hannun Pulisic ta rama kwallon kuma ta yi kari ta hannun Aubameyang.   Bayan kammala Wasan, Arsenal ta dauki Kofin Karo na 14 kenan a tarihi. Yan wasan sun ta nuna Murnar su a Fili inda har suka shiga cikin dakin canja kaya ana ta murna.   Lacazette da Aubameyang sun dauki wani hoto da kofin na FA da ya matukar kayatar.
Arsenal ta lashe kofin FA Cup bayan sun ba Chelsea kashi 2-1, yayin da Aubameyang yaci gabadaya kwallayen

Arsenal ta lashe kofin FA Cup bayan sun ba Chelsea kashi 2-1, yayin da Aubameyang yaci gabadaya kwallayen

Uncategorized
A yau ranar sati daya ga watan augusta aka buga wasan final na gasar FA Cup tsakanin Arsenal da Chelsea, kuma tawagar Mikel Arteta tayi nasarar ba Chelsea kashi har 2-1. Pierre Emerick Aubameyang ne yayi nasarar ciwa Arsenal gabadaya kwallayen guda biyu, yayin da yaci kwallo guda kafin aje hutun rabin lokaci kuma ya kara wata bayan an dawo daga hutun. Shima Christian Pulsic yayi nasarar ciwa Chelsea kwallo guda amma sai dai ya bar wasan saboda rauni. Pulsic yasa tawagar Lampard sun fara jagorantar wasan cikin minti biyar, amma Aubameyang ya ramawa Arsenal kwallon kuma ya kara wata a minti na 67. Kovakic ya samu yalon kati na biyu bayan ya bugi Granit Zhaka wanda hakan yasa aka ba shi jan kati kuma Chelsea suka gama wasan da yan wasa goma. Sakamakon wasan na nufin cewa ...
Arsenal da Chelsea zasu kara a wasan Final na FA Cup karo na uku, bayan Arsenal taci wasannin biyu da suka gabata

Arsenal da Chelsea zasu kara a wasan Final na FA Cup karo na uku, bayan Arsenal taci wasannin biyu da suka gabata

Wasanni
Chelsea ta zamo kungiya ta farko data ci Manchester United a wasa na gasar premier lig tun bayan kungiyar Burnley sun ci su a watan janairu, United sun buga wasanni 19 ba tare da an cire su ba amma Chelsea ta basu kashi jiya da ci uku da daya. Kungiyar Chelsea ta cire Manchester United a gasar FA Cup karo na shida wanda suka hada da uku cikin hudu da suka gabata, kungiyar Arsenal ce kadai ta cire Manchester United a gasar fiye da Chelsea, yayin da tayi hakan sau bakwai. Chelsea da Arsenal zasu kara a wasan Final na gasar FA Cup karo na uku a ranar daya ga watan augusta, kuma Arsenal ne suka yi nasara a wasannin Final din guda biyu da suka gabata a shekara ta 2002 da 2017. Chelsea sun kai wasannin Final na gasar FA Cup sau 14 kuma kungiyar Arsenal ce tafi gabadaya kungiyoyin gasar ...
Bidiyon Leicester City 0-1 Chelsea: Ross Barkley ya taimakawa Chelsea sun yi nasarar zuwa wasan semi final na gasar FA Cup

Bidiyon Leicester City 0-1 Chelsea: Ross Barkley ya taimakawa Chelsea sun yi nasarar zuwa wasan semi final na gasar FA Cup

Wasanni
Sakamakon wasan ya kwantar da hankalin Frank Lampard bayan ya firgita kafin aje hutun rabin lokaci saboda leicester City sun fi Chelsea kokari a lokacin, duk da cewa Christian Pulisic ya kai wani hari mai kyau amma bai ci kwallon ba. Duk da kokarin da Leicester suka yi dai ko kwallo daya basu ci ba, yayin da shi kuma babban kochin Chelsea ya canja mutane uku kuma suka fara yin kokari bayan an dawo daga hutun rabin lokacin. Daya daga cikin yan wasan daya yiwa canji Barkley shine yayi nasarar kubutar dasu a hannun leicester City. Tammy Abraham yaci wata kwallo amma alkalin wasa yace Offside ne, kuma duk da haka sai da suka cigaba da yin kokari har suka ci kwallo a minti na 63. Yanzu Chelsea sun kai wasan semi final na FA Cup karo 24 kuma sun yi nasara a wasannin su guda biyar da du...
Na saki Kari:Ighalo ya Karyata hasashen da nai masa cewa bazai tabuka abin azo a gani ba>>Ferdinand

Na saki Kari:Ighalo ya Karyata hasashen da nai masa cewa bazai tabuka abin azo a gani ba>>Ferdinand

Wasanni
Tsohon dan wasan baya na Manchester United Rio Ferdinand yace odion ighalo ya karyata shi kan hasashen da yayi na cewa bai cancanci wasa a kungiyar ba Ferdinand yana magana ne a BT Sport, ayayin da ighalo ya jefa kwallaye 2 a raga lokacin da suka yi nasarar wasan su da Derby county 3 : 0 a zagaye na biyar na gasar FA Cup. Anyi tambayoyi da yawa, ayayin da Ole Gunnar Solskjaer ya aro dan wasan gaba na Nigeria na tsawon watanni shida  a watan janairu. Masu sharhi suna cewa ighalo wanda ya taba bugama Watford wasa na Premier League bai kai matsayin wasa a Manchester United ba. Amma,Ighalo mai shekaru 30 a yanzu haka yana da kwallaye 3 a wasanni biyu kacal daya buga a garin. Rio Ferdinand yace yawacin mutane da nima kaina muna tunani akan Ighalo, tayaya ya dace da irin ...

Dan kwallon Najeriya Odion Ighalo ya kafa sabon tarihi a wasan da Man United ta wa Derby 3-0

Wasanni
Tauraron dan kwallon Najeriya dake bugawa Manchester United wasa a matsayin aro, Odion Ighalo ya ciwa kungiyar tashi kwallaye 2 a karawar da suka yi a daren Alhamis na gasar daukar kofin FA da kungiyar Derby County. https://twitter.com/EmiratesFACup/status/1235663987381088257?s=19 Shaw ne ya fara ciwa Man United kwallo gun kamin a je hutun rabin lokaci inda Ighalo ya kara kwallo ta 2. Bayan dawowa hutun rabin lokacine Ighalo ya kara cin kwallo ta 3 wanda a haka aka tashi wasan. https://twitter.com/EmiratesFACup/status/1235676393909800960?s=19 Da wannan sakamako, Man United ta kai ga matakin wasan Quarter Finals inda zata hadu da Norwich.   Da kwallaye 2n da yaci, Ighalo ne ya karbi kyautar gwarzon dan wasan. Sankan ya kafa tarihin zama dan Najeriya na farko da ya ciw...