
Wolves ta tabbatar da siyan Fabio Silva a farashin da bata taba siyan wani dan wasa ba
Tauraron dan wasan Portugal, Fabio Silva mai shekaru 18 ya saka hannu a takaddun sabon kwantirakin da kungiyar Wolves ta yi har na tsawon shekaru biyar bayan ta siyo a farashin yuro miliyan 35 daga kungiyar Porto wanda hakan yasa yanzu ya zamo dan wasa mafi tsada da kungiyar ta siya a tarihi bayan Raul data siya a farashin yuro milian 30.
Silva ya zamo dan wasa na farko da kungiyar Wolves ta siya a wannan kakar bayan shugabanm kungiyar Nuno Espirito Santo ayi kira ga sauran shwagabannin kungiyar cewa ya kamata su karawa tawagar karfi bayan Sevilla ta cire su a gasar Europa League a watan augusta.
Dan wasan Portugal mai shekaru 18 yayi nasarar cin kwallo guda a wasanni 12 daya bugawa kungiyar Porto a kakar wasan bara na gasar Premeira Liga, kuma a 2019 yayi nasarar zira kwallaye 33 ...