fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Fadar shugaban kasa

Shugaba Buhari ya gana da Abdulsalam Abubakar

Shugaba Buhari ya gana da Abdulsalam Abubakar

Siyasa, Uncategorized
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gana da tsohon Shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar a Fadarsa da yammacin yau, Juma'a.   Hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ne ya  bayyana haka amma be fadi dalilin ganawar tasu ba.   Saidai ana tsammanin bata rasa nasaba da matsalar tsaron dake fuskantar Najeriya da kuma kiraye-kirayen Raba kasa.   A baya dai hutudole.com ya ruwaito muku cewa kakakin Shugaban kasar, Malam Garba Shehu yace, Babu wanda ya isa ya kifar da Gwamnatin Shugaba Buhari
Daga yanzu duk wani ma’aikacin gwamnati idan yana son fita kasar waje jinya to ya fita da kudinsa ba na gwamnati ba>>Majalisa ta Murza gashin baki

Daga yanzu duk wani ma’aikacin gwamnati idan yana son fita kasar waje jinya to ya fita da kudinsa ba na gwamnati ba>>Majalisa ta Murza gashin baki

Siyasa
Majalisar tarayya ta bayyana cewa daga yanzu duk wanda zai fita neman magani kasar waje to ya fita da kudinsa bana Gwamnatin tarayya ba.   Majalisar ta yi wannan maganane a yayin da sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar ya je kare kasafin kudin shekarar 2021. Vanguard ta ruwaito cewa daga Biliyan 19.7 da aka amincewa fadar shugaban kasar, Biliyan 1.3 na Asibitin fadar ne, saidai sakataren yace sun yi kadan.   Da yake magana akan kudin da aka warewa Asibitin, shugaban kwamitin dake kula da raba daidai na mukaman Gwamnati da kuma dangantaka tsakanin ma'aikatu, Sanata Danjuma La'a ya bayyana cewa zasu amince da kasafin kudin amma maganar gaskiya itace ya kamata idan maganar rashin lafiyar shugaban kasa ta tashi a rika dubashi a Asibitin kamin idan ya zama do...
Masu son tada zaune tsayene suka dauki Bidiyon Oshiomhole da Gambari na maganar kama wasu ‘yan Siyasa>>Gwamnatin Tarayya

Masu son tada zaune tsayene suka dauki Bidiyon Oshiomhole da Gambari na maganar kama wasu ‘yan Siyasa>>Gwamnatin Tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa wasu masu son tada zaune tsaye ne suka dauka tare da watsa bidiyon tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.   An dai dauki Bidiyon ne inda aka ji shuwagabannin a fadar shugaban kasa suna maganar kama wasu mutane. Hutudole ya ruwaito muku cewa an yi bidiyonne yayin ziyarar da Adams Oshiomhole ya kai fadar shugaban kasar. Daga baya an yi ta cece-kuce akan Bidiyon inda wasu da dama suka yi magana kan cewa wasu mutanene a jihar Edo da ake shirin yin zaben gwamna za'a kama.   PDP a martanin da ta yi kan wannan batu ta yi kira da a kama shuwagabannin da tuhumar su kan wanan Bidiyo inda kuma tace dalilin da yasa APC ke tunanin kama wasu 'yan adawa shine ta ga ba nasara ...
Bamu da hannu a gayyatar da DSS tawa Ghali Na’abba, ‘Yan Siyasa na gaske kadai muke kulawa>>Fadar shugaban kasa

Bamu da hannu a gayyatar da DSS tawa Ghali Na’abba, ‘Yan Siyasa na gaske kadai muke kulawa>>Fadar shugaban kasa

Siyasa
Fadar shugaban kasa ta yi magana akan yanda ake danganta kalaman da tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba yayi akan gwamnati da gayyatar da DSS ta masa.   Da yake magana da manema labarai a jiya, Lahadi, me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, babu alaka tsakanin gayyatar da DSS tawa Ghali Na'abba da kalaman da yayi akan gwamnati. Hutudole ya fahimci Garba yace 'yan Siyasa na gaske ne idan suka yi magana take daukar hankalin gwamnati kuma ta mayar da martani. Yace amma maganar da Ghali na'abba yayi bata dauki hankalin gwamnatin ba dama sauran 'yan siyasa na gaske. Hutudole ya ruwaito Garba na cewa 'yan Siyasa masu kokarin daukar hankalin mutane basa damun Gwamnati.   Ya baiwa na'abba shawarar ya daina alakanta Gwamnat...
Ba dan kuri’ar Yarbawa ba da Buhari bai zama shugaban kasa ba>>Tony Momoh

Ba dan kuri’ar Yarbawa ba da Buhari bai zama shugaban kasa ba>>Tony Momoh

Siyasa
Tsohon Ministan yada Labarai Tony Monoh ya bayyana cewa ba dan kuri'ar yankin Yarbawa ba da shugaba Buhari bai zama shugaban kasa ba.   Ya bayyana hakane a hirar da Independent ta yi dashi inda yace APC hadewar ACN ta bangaren yarbawa da CPC ce da kuma wasu da suka bar PDP. Yace a shekarar 2003 shugaba Buhari ya samu kuri'a Miliyan 12 hakanan a shekarar 2011 ya kara samun kuri'a miliyan 12.   Yacs bayan da aka hade guri gida da sauran jam'iyyi, Shugaba Buhari ya samu kuri'a Miliyan 15, yace to kaga wannan Miliyan 3 daga bangaren yarbawa ta fito wadda ba dan ita ba da shugaban bai ci zabe ba.
Da Dumi-Dumi: An gano wanda ya jagoranci tafka sata a Fadar shugaban kasa

Da Dumi-Dumi: An gano wanda ya jagoranci tafka sata a Fadar shugaban kasa

Uncategorized
Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Aso Villa na cewa jami'an 'yansandan farin kaya,DSS dana hukumar binciken manyan Laifuka FCID sun fara bincike dan zakulo wanda ake zargi da shiga Ofishin hukumar dake saka ido kan harkokin kudi a kasarnan, NFIU suka sace Kwamfutoci da kuma lalata wasu bayanai.   Lamarin satar ya farune a daren Alhamis din da ta gabata inda da Safiyar Juma'a aka tashi da wannan gagarumin abin mamaki. Mutane 6 ne suka aikata wannan ta'asa wanda kuma kyamarar CCTV ta dauki hotunansu, bayan duba bidiyon kyamarar ta CCTV data nuna yanda suka yo satar, an gano cewa wani babban jami'in dansanda me mukamin Superintendent ne ya jagoranci wannan sata wanda kuma tuni ya ranta a na kare.   Saidai jami'an tsaron sun fara bin sahunsa da wanda suka taimaka...