
Mutuwar Fadila(Lollipop) Allah ne ya karbi Addu’arta>>Cewar Mahaifin Marigayiyar
Rahotanni sun bayyana cewa ciwon zuciyane yayi silar rasuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Fadila Muhammad da aka fi sani da Lollipop.
A ranar Juma'a 28 ga watan Augusta ne da misalin Karfe 11 na darene Lollipop ta rasu a cikin motar Mahaifinta tana da shekaru 27, kamar yanda hutudole ya samo muku daga Mujallar Fim.
Dama tana fama da ciwon Zuciya wanda kuma a ranar shine yayi mata tasowar Karshe, ta rasu a motar mahaifinta yayin da yake hanyar kaita Asibiti.
A hirar da yayi da majiyar tamu, Malam Muhammad ya ce, "Wannan rashi da mu ka yi babu abin da zan ce sai Allah ya jiƙan ta da rahama, Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare ta" Ya na faɗin haka sai ya fara kuka.
Ya ci gaba da cewa: "Wannan yarinya babu abin da zan ce mata sai Allah ...