fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Tag: Falalu A. Dorayi

Idan dai Jira za’a rika yi sai sun kawo hari a je a rama, hakan zai ci gaba da fito da gazawar Gwamnati>>Falalu A. Dorayi

Idan dai Jira za’a rika yi sai sun kawo hari a je a rama, hakan zai ci gaba da fito da gazawar Gwamnati>>Falalu A. Dorayi

Tsaro
KANKARA KATSINA In dai jira za’a cigaba da yi har sai sun kawo hari sannan aje a rama, to hakan zai cigaba da fito da gazawar gwamnati kenan. Ina tabbas za’a iya kawar dasu.   Yan bindiga a jiya daddare jiya sun shiga Wata makaranta a kankara ta jihar Katsina da muggan makamai. Bayan hallaka mai lura da makarantar sun sace dalibi masu yawa sun yi gaba dasu.   Ku saurari wani Video da WD Hausa suka saki, Kaji muryoyin iyayen yaran da aka dauka, kaji abin tada hankali.   Jami’an tsaronmu a da, har wasu kasashen makotanmu suke kai agajin zaman lafiya. Saboda karfinsu da kwarewar aiki. Abin mamaki ga wuta ta tashi tana neman cinye mutane da dukiyoyi da zaman lafiya. Kisan wutar na neman zama siyasa. SIYASA DA RAYUKAN mutane ba zai haifar mana Abin alkair...
Shiru akan Barna kamar Amincewa da itane>>Falalu A. Dorayi yayi jan hankali kan shigar Banza

Shiru akan Barna kamar Amincewa da itane>>Falalu A. Dorayi yayi jan hankali kan shigar Banza

Nishaɗi
Bayan wasu hotunan tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau da suka jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta, Kafafen zada zumuntar sun dauki dumi inda aka rika cece-kuce akansu. Da dama da suka bibiyi lamarin sun bayyana cewa dalilin hakan an yiwa fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad(SAW) batanci wanda hakan ya jawo Rahama Sadau ta cire daya daga cikin hotunan wanda ya nuna gadon bayanta, sannan ta nesanta kanta da kalaman batanci da akawa Addini.   Bayan faruwar lamarin, Falalu A. Dorayi yayi magana akan yin Nasiha ba da tozarci ba da kuma illar shigar banza. Duk da dai bai kira suna ba a cikin Nasihar tasa, da dama sun yi amannar cewa wannan Nasiha tasa bata rasa nasaba da hotunan na Rahama Sadau.   A cikin Nasihar tasa me kashe jiki, Falalu A. Dorayi ya bayyana ...
Idan Kun Shirya mun Shirya>>Falalu A. Dorayi akan Zanga-zangar Arewa

Idan Kun Shirya mun Shirya>>Falalu A. Dorayi akan Zanga-zangar Arewa

Siyasa
Falalu A. Dorayi yayi magana akan yon zanga-zanga a Arewa yayin da yake baiwa wani amsa ta shafinsa na sada Zumunta.   Falalu yayi kiran cewa a kawo karshen Boko Haram da 'yan Bindiga, sai wani yake ce masa zanga-zanga ya kamata su fito ba'a shafukan sada zumunta ba. Saidai Falalun ya bayyana masa cewa indai sun shirya suma a shirye suke dan Arewar ba ta 'ya  Fim bane su kadai.   Zanga-zangar da 'yan Kudu suka fito suka yi ta zaburar da 'yan Arewa akan kwaikwayonsu kan matsalolin dake damjn yankin. https://www.instagram.com/p/CGQZJxRD3pw/?igshid=18un2oxwbu1jm  
Mu ribaci kwana goman farko na Zul Hijja>>Falalu Dorayi

Mu ribaci kwana goman farko na Zul Hijja>>Falalu Dorayi

Nishaɗi
Fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi ya yi kira da Musulmi su dage wajen ribatar kwana goman farko na watan Zul Hijja saboda matsayin kwanakin a wajen Allah.   Falalu ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana kwanakin a matsayin masu daraja da albarka. Ya ce manzon Allah ya nuna cewa babu kwanaki da aikin alheri ya fi soyuwa a cikinsu irin wadannan ranaku.   “Kwana 10 Zul Hijjah kwanaki ne masu daraja da albarka, saboda matsayinsu a wajan Allah.   “A cikinsu Allah ta’ala Ya cika addini, kuma da cikar addini ne imani ya yi karfi sai munafurcin zuciya ya mutu.   “Da karfin imani mutum ke cin nasara a kan zuciyarsa wadda take ba shi umarni zuwa mummunan aiki.   “Mu yawaita ayyukan alheri irins...
Duk wanda ya bar tarbiyyar ‘ya’yansa a hannun Talabijin ba zai ga daidai ba,Hukuncin kisa ne ya kamata akan masu Fyade>>Falalu A. Dorayi

Duk wanda ya bar tarbiyyar ‘ya’yansa a hannun Talabijin ba zai ga daidai ba,Hukuncin kisa ne ya kamata akan masu Fyade>>Falalu A. Dorayi

Nishaɗi
Bayanin Tauraron fina-finan Hausa kuma babban Darakta, Falalu A. Dorayi akan Fyade yace ba saka kayan Tsiraicine kadai ke sanya Fyade ba inda ya bada misalai da dama.   Falalu yace hukuncin kisa ya kamata a yankewa me Fyade kuma a yishi a gaban jama'a.   R A P E (F Y A D E) Fyade dabi’a ce mummuna abar kyama da take nema ta zama ruwan dare a cikin al’ummar mu. A fahimtar wasu mutane, dalilansu na abin da yake haifar da FYADE sunce shigar tsiraici ce.     Kashi 85% cikin 100 ayyukan FYADE da ya faru a yankunanmu, wanda muka ji da wanda muka gani da wanda muka karanta da wanda aka bani labari, ya faru ne ba tare da saka kaya masu fidda tsiraici ba.     Masu aikata wannan dabi’a zaka rasa me suke nema, domin basu kyale duk wan...
Babu wani abu da zai faru a doran Duniya babu sanin Allah>>Martanin Falalu A. Dorayi kan Sauke Sarki Sanusi

Babu wani abu da zai faru a doran Duniya babu sanin Allah>>Martanin Falalu A. Dorayi kan Sauke Sarki Sanusi

Nishaɗi
Tauraron me bayar da umarni na fina-finan Hausa kuma Jarumi, Falalu A. Dorayi ya bayyana ra'ayinsa kan sauke Sarki Muhammad Sanusi II daga sarauta.   A sakon da ya rubuta a shafinsa na sada zumunta Falalu yayi tuni da Imani da Kaddara.   Fafalu yayi rubutu kamar haka:   Babu wani abu da zai faru a doran duniya babu sanin Allah, Tsakanin Alkairi da Akasin haka. Tsakanin wanda aka cire da wanda aka dora dukkan su suna rayuwa ne akan Littafin Kaddara, a rubuce yake sai hakan ya kasance tare dasu. Yana cikin tarbiyar Addini yadda da kaddara mai kyau da mara kyau, a kano kaddara 2 ce ta sauka, a bangare daya kukan bakin ciki a ke, a daya bangaren kuka farin ciki a ke. Kuma hakan zatai ta faruwa a rayuwar duk wanda ya kadaita Allah. Yau farin ciki gobe akasi...