fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Faransa

Mbappe ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga yayin da Faransa ta lallasa Kazakhstan daci 2-0 a wasannin cancantar buga gasar kofin duniyan shekarar 2022

Mbappe ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga yayin da Faransa ta lallasa Kazakhstan daci 2-0 a wasannin cancantar buga gasar kofin duniyan shekarar 2022

Wasanni
Kasar Faransa tayi nasarar lallasa Kazakhstan daci 2-0 ta hannun Dembele da Sergiy Mailiy wanda yaci gida tun kafin aje hutun rabin lokaci, kafin daga bisani Mbappe ya barar masu da bugun daga kai sai mai tsaron raga. Nasarar da Faransa tayi tasa ta dare saman teburin Group D fa maki hudu na inda ta wuce Bosnia wadda zasu da ita rabar laraba da kuma Ukraine da Finland. Tauraron dan wasan Manchester United, Anthony Martial ya samu rauni a wasan wanda hakan yasa har aka yi musayar shi da wani dan wasan. The world champions built their win in the first half with Sergiy Maliy's own goal adding to Dembele's opener before Kylian Mbappe missed a second-half penalty. A baya dai, hutudole.com ya ruwaito muku yanda Real Madrid ke son sayar da manyan 'yan wasanta dan sayen Mbappe da...
Kasar Faransa zata kai samame Masallatai da yiyuwar Kullesu

Kasar Faransa zata kai samame Masallatai da yiyuwar Kullesu

Uncategorized
Ministan cikin gida na Faransa ya ce gwamnatin ƙasar za ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri da ba a taɓa ganin irinsa ba kan masallatan da ake zargi na karfafa tsatsauran ra'ayin addinin Islama. Mista Gerald Darmanin ya ce za a fara ne da masallatai 76 a cikin kwanaki masu zuwa, wataƙila ma a rufe wasunsu idan ta kama. Wannan dai shi ne sabon matakin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta dauka bayan hare-haren da ke da alaƙa da na masu tsatsauran ra'ayi a kasar. A kwanakin baya ne aka fille kan malamin da ya nuna wa 'yan ajinsa zanen Annabi Muhammad, wanda ake kallo a matsayin izgilanci ga addinin Islama da mabiyansa. Zane-zanen da wasu Faransawa ke yi tare da alaƙantasu da wani addini na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a duniya, har ta kai ga ƙasashen ...
Da Duminsa:Shugaban Kasar Faransa ya sassauto kan kalaman Batanci ga Annabi(SAW)

Da Duminsa:Shugaban Kasar Faransa ya sassauto kan kalaman Batanci ga Annabi(SAW)

Siyasa
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da a baya ya goyi bayan batanci ga Annabi(SAW) da aka yi a wani zane da mujallar Charlie Hebdo ta yi a yanzu ya sassauto.   A wata hira da aka yi dashi a gidan Jaridar Aljazeera ya bayyana cewa yanzu ya fahimci cewa zanen Annabi(SAW) da aka yi ya batawa musulmi rai.   Saidai yace hakan ba hujja bace da ya kamata a fake da ita wajan kai hare-hare,  kamar yanda kamfanin dillancin labaran AFP ya bayyana.   #BREAKING French President Emmanuel Macron expressed understanding that cartoons of the prophet Mohammed could shock Muslims, but said that this could never be used to justify violence, in an interview with Al-Jazeera to be broadcast in full on Saturday https://twitter.com/AFP/status/1322525431082504193?s=19
Hotuna:Yanda aka yi Arangama a kasar Ingila tsakanin ‘yansanda da Musulmai da suka fito neman a girmama manzon Allah(SAW) da Allah wadai da kasar Faransa

Hotuna:Yanda aka yi Arangama a kasar Ingila tsakanin ‘yansanda da Musulmai da suka fito neman a girmama manzon Allah(SAW) da Allah wadai da kasar Faransa

Siyasa
Musulmai a Birnin Landan na kasar Ingila su  fito a yau inda suka je ofishin jakadancin Faransa dake Landan din suka yi zanga-zangar neman a girmama Annabi(SAW).   Musulman sun kuma dauki kwalaye da ke bayyana shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron a matsayin shaidani, wasu kuma na kira a gareshi ya girmama manzon Allah(SAW).   Saidai daga baya 'yansanda sun bukaci masu zanga-zangar su watse kuma sun watse din amma an samu kalilan da suka ki tafiya, Hukumar 'yansandan birnin ta sanar da kama mutane 3 a zanga-zangar.   Hakanan kuma ofishin jakadancin kasar Faransar dake Landan ya bayyana cewa kasarsu ba zata canja hali ba kan bayar da 'yancin fadar albarkacin baki ba. Macron has become the focal point of Islamic fury after defending Charlie Hebd...
Musulunci ba Addinin ta’addanci bane:Mesut Ozil yayi Allah wadai da kashe-kashen kasar Faransa

Musulunci ba Addinin ta’addanci bane:Mesut Ozil yayi Allah wadai da kashe-kashen kasar Faransa

Siyasa
Tauraron dan kwallon Kasar Jamus dake bugawa Arsenal wasa, Mesut Ozil ya bayyana Cewa Addinin Musulunci ba addinin ta'addanci bane.   Ya bayyana haka ne a shafinsa na sada zumuntar Twitter inda ya saka Ayar Qurani dake cewa, duk wanda ya kashe rai ba tare da hakki ba, kamar ya kashe dukkan al'umma ne haka duk wanda tseratar da rai, kamar ya tseratar da dukkan Al'umma ne. Suratul Ma'idah 5:32. https://twitter.com/MesutOzil1088/status/1322109242908774401?s=19 Hakan na zuwane bayan da aka samu kashe wani malamin kasar Faransa da ya nunawa dalibansa hotunan zanen batanci da akawa Annabi(SAW).   Hakanan kuma an kashe wasu mutane 3 ta hanyar hari da wuka a birnin Nice na kasar ta faransa a cocin Notre dame.  Shugaban kasar Faransa na ci gaba da shan suka daga kasashen...
Fir’auna ma Tarihi ya zama>>Sarkin Waka ya gayawa Shugaban Faransa

Fir’auna ma Tarihi ya zama>>Sarkin Waka ya gayawa Shugaban Faransa

Siyasa
Tauraron mawakin Hausa kuma jarumin Fina-finan Hausa,  Nazir Ahmad Sarkin Waka ya bayyanawa shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron cewa Fir'auna ma Tarihi ya zama.   Sarkin waka ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, Ku suwa, Karamin Arne, ga ka nan ga me addinin, Firauna ma Tarihi ya zama. https://www.instagram.com/p/CG-Rf4aJZBh/?igshid=1e45k8sd66a6z   Shugaban Faransa na ci gaba da shan suka sosai daga wajan Musulmai saboda Goyon bayan batanci ga Annabi(SAW) da yayi.
Kasar Faransa tace ta daura damarar yaki da Akidun Addinin Islama

Kasar Faransa tace ta daura damarar yaki da Akidun Addinin Islama

Siyasa
Ministan cikin gida na Faransa Gerald Darmanin ya ce Faransa na yaki da akidun Islama, bayan kashe wasu mutane uku a wata coci da ke kudancin birnin Nice. Ya yi gargadin kara samun irin wadannan hare-hare, sai dai ya jaddada cewa Faransa ba ta yaki da wani addini. Jagoran 'yan adawar kasar Marine Le Pen ta yi kira ga gwamnati ta bijiro da dokokin gaggawa don tasa keyar masu kaifin kishin Islama zuwa kasashensu na ainihi. Shugaba Emmanuel Macron zai sake gudanar da wani taro na majalisar tsaro don tattaunawa game da harin Nice da kullen korona, wanda ya fara aiki da tsakar dare. Wanda ake zargi da kisan na birnin Nice na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan 'yan sanda sun harbe shi.
Shugaban Kasar Faransa Bai waye ba kuma Musulmai nada damar kashe ‘yan kasarsa>>Tsohon shugaban Malaysia

Shugaban Kasar Faransa Bai waye ba kuma Musulmai nada damar kashe ‘yan kasarsa>>Tsohon shugaban Malaysia

Siyasa
Tsohon Firaiministan Malaysia,  Mahathir Mohamad ya bayyana cewa a shekarun baya, kasar Faransa ta wa Musulmai kisan kiyashi.   Yace dan haka musulman na da ikon ramuwar kisan da aka musu. Yace ya kamata kasar Faransa ta koyawa mutanenta girmama addinin wasu koda kuwa suna da 'yancin fadar albarkacin bakinsu.   Yace baya goyon bayan kisan malamin da aka yi wanda ya nunawa dalibansa hotunan batancin da akawa Annabi(SAW) amma a kowane addini ana samun masu kisan mutane.   Ya kuma zargi shugaban kasar Faransa da cewa mutum ne dake da hali irin na kauyawa wanda bai waye ba.   Shugaba Mahathir ya bayyana hakane ta shafinsa na Twitter amma tuni ya goge sakon. Saidai kasar Faransa ta nemi kamfanin Twitter ya kulle shafin shugaba Mahathir ko kuma a kalle...