fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Farashin kayan Abinci

Hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 13.71 a watan Satumba, mafi tsada tun shekarar 2016

Hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 13.71 a watan Satumba, mafi tsada tun shekarar 2016

Siyasa
Kididdigar auna hauhawar farashin kayan abinci ta nuna cewa an samu tashin farashin da kasho 13.71 cikin 100 a watan Satumba 2020. Wannan ya nuna karin kaso 0.49 cikin dari wanda ya dara wanda aka samu a watan Agusta 2020-13.22. Dangane da rahoton watan Satumba na CPI / hauhawar farashi da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, a kan wata-wata, adadin ya karu da kashi 1.48 a watan Satumbar 2020. Wannan ya nuna an sami karin 0.14  fiye da wanda aka samu a watan Agusta 2020 (1.34). Hauhawar farashin kayan abinci ya tsaya a kashi 16.66 a watan Satumba na 2020 daga kashi 16.00 a watan Agusta 2020. Babban Hauhawar farashin a kaso 10.58 bisa dari a Satumba 2020 daga 10.52 bisa dari a watan Agusta 2020. “A bayanan wata-wata farashin ya karu da kashi 1.48 a watan Satumbar 2020. Wan...
Farashin Kayan Abinci sun fado a kasuwar Saminaka

Farashin Kayan Abinci sun fado a kasuwar Saminaka

Kasuwanci
Rahotanni daga kasuwar Saminaka dake jihar Kaduna na cewa farashin kayan Abinci sun fadi da kaso 30 cikin 100.   Saminaka na daya daga cikin manyan garuruwan dake samar da Masara a Najeriya. Daily Trust ta samo cewa farashin Buhun sabuwar Masara Kilogiram 100 da a baya ake sayar dashi akan farashin 15,000 yanzu ya zama 10,000 zuwa 12,000.   Hakanan sabuwar shinkafa da a baya ake sayar da ita akan farashin 49,000 zuwa 50,000 yanzu ana sayarwa akan farashin 32,000 zuwa 35,000.   Farashin Mudun Shinkafa 'yar gida yanzu ya koma 450 daga 750. Sai kuma na masara ya sauka daga 300 zuwa 150.   Shugaban 'yan kasuwar, Manu Isa ya bayyana cewa farashin kayan abincin ya sauka.
Daga shekaru 5 da shugaba Buhari ya hau mulki zuwa yanzu, farashin kayan Abinci sun tashi da kaso 108 duk da zuba Tiriliyan 2 a harkar noma>>Nairametrics

Daga shekaru 5 da shugaba Buhari ya hau mulki zuwa yanzu, farashin kayan Abinci sun tashi da kaso 108 duk da zuba Tiriliyan 2 a harkar noma>>Nairametrics

Uncategorized
Rahotannin da shafin dake kididdiga kan harkar kasuwanci da kudi a Najeriya, Nairametrics na cewa, daga shekarar 2015 zuwa yanzu da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya hau mulki farashin kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi da kaso 108 cikin 100.   Hakarar darajar Naira ta fadi da kaso 49 cikin 100. Hakan na zuwane duk da Makudan kudaden da Gwamnati ta kashe akan harkar noma da Rahoton yace sun kai Naira Tiriliyan 2 cikin shekaru 5 din da suka gabata. Saidai Rahoton yace wasu daga cikin dalilan dake sanya tsadar farashin kayan abincin ba laifin gwamnati bane. Misali Rahoton ya kawo matsalar dillalai da matsalar jigilar kayan abincin zuwa kasuwanni da matsalar guraren ajiya da matsalar rashin samun yabanya irin wadda sauran kasashen Duniya ke samu a gonakin Najeriya, amb...
Ministar Kudi ta karyata fadar shugaban kasa, tace farashin kayan abinci na tashi

Ministar Kudi ta karyata fadar shugaban kasa, tace farashin kayan abinci na tashi

Siyasa
Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta karyata fadar shugaban kasa inda tace farashin kayan abinci na tashi.   A baya dai a wata hira da yayi da Channelstv,  kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa kayan abinci na saukowa inda har ya bada Misali da Kano. Saidai a nata bangaren, Ministar Kudin, Zainab Shamsuna da take amsa tambayoyi daga manema labarai tace gaskiyane farashin kayan abincin na tashi amma kuma ba lallai su ci gaba da tashi ba saboda yawancin manyan motocin dake kai kayan abincin ga masu saye na amfani da gas ne.
Yawancin ‘yan Najeriya kudadensu wajen sayen abinci yake tafiya>>Bincike

Yawancin ‘yan Najeriya kudadensu wajen sayen abinci yake tafiya>>Bincike

Tsaro
Wani Rahoto da kamfanin The SB Morgen na kasar Amurka ya wallafa, ya bayyana cewa kaso 63 na 'yan Najeriya kudinsu akan sayen Abinci yake karewa.   Kamfanin wanda ya kware wajan samar da bayanan tattalin Arziki a Africa ya bayyana cewa, Mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari za'a rika tunashi da tsadar abincin da ya kawowa kasar. Hutudole ya fahimci Rahoton yace a lokacin da shugaba Buhari ya karbi Mulki farashin kayan abinci basu kai yanzu tsada ba.   Rahoton yace tsare-tsare marasa tasiri da gwamnatin ta dauka kan tattalin arziki na daya daga cikin dalilin da yasa farashin kayan abinci ke hauhawa inda kaso 37 cikin 100 na 'yan kasar ne kawai ke samun rarar kudi bayan siyen kayan abinci.   Hakanan Binciken ya kuma bayyana matsalar tsaro a matsayin daya dag...