
Na fada na sake fada kuma bazan taba canjawa ba, Mulkin Obasanjo ya fi na Buhari >>Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi
Farfesa Ango Abdullahi wanda shine shugaban kungiyar Dattawan Arewa yayi magana akan cewa ya kamata Najeriya ta manta da batun mulkin karba-karba tsakanin Arewa da kudu.
Ango Abdullahi ya kuma bayyana cewa baya cikin wanda ke murnar cikar shekara 5 da mulkin shugaban kasa,Muhammadu Buhari kamar yanda hutudole ya jiwoshi a hirar da Sunnews suka yi dashi.
Ya kuma bayyana cewa shi a wajanshi har yanzu 1 ga watan October Itace ranar 'yancin Najeriya da Dimokradiyya ba wai Yuni 12 ko Mayu 29 ba.
Ya kuma zargi 'yan Jarida da dewa basa taimakawa ci gaban harkar Dimokradiyya inda ya zargesu da cewa sun zama 'yan amshin shatar 'yan jarida.