
“Najeriya ba zata samu cigaba ba saboda gwamnati bata gudanar da mulkin kasar yadda ya kamata”>>Jega
Tsohon shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe na kasa wato Attahiru Jega ya bayyana cewa gwamnati bata gudanar da mulki yadda ya kamata a yanzu.
Ya bayyana hakan ne a babban taron da jam'iyyar PRP ta gudanar ranar sati, inda yace babu kasar data taba samun cigaba face ta samu gwamnati mai gudanar da mulki yadda ya kamata.
Saboda haka ne yake bukatar mutane dasu tashe tsaye domin akwai gagarumin aiki a gabansu, kuma tabbas zasu iya magance matsalar idan suka hada kai.
Jam'iyyar PRP a babban taron data gudanar ta sake zabar Alhaji Falalu Bello domin ya cigaba da shugabancinta.