fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Farfesa Ibrahim Gamabari

Safar Dambe da Addu’a kake bukata fiye da takunkumin Rufe Hanci>>Sanata Shehu Sani ya gayawa Sabon Shugaban ma’aikatan Buhari

Safar Dambe da Addu’a kake bukata fiye da takunkumin Rufe Hanci>>Sanata Shehu Sani ya gayawa Sabon Shugaban ma’aikatan Buhari

Siyasa
A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatansa.   Ibrahim Gambari ya maye gurbin marigayi Abba Kyari da cutar Coronavirus/COVID-19 ta kashe kuma mutane da yawa ciki hadda Bukola Saraki da Atiku Abubakar sun taya Gambari Murna.   A sakon taya Murna da Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya aikewa farfesa Gambari ya bayyana cewa yana tayashi murna amma fa Addu'a da Safar Hannu ta Dambe ce yake bukata fiye da Takunkumin rufe fuska. https://twitter.com/ShehuSani/status/1260578840906289160?s=19 Mutane da dama dai sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan wannan lamari.
“Al’hakina shine in Kai rahoto ga shugaban kasa ba ga jama’a ba>> Farfesa Gambari

“Al’hakina shine in Kai rahoto ga shugaban kasa ba ga jama’a ba>> Farfesa Gambari

Siyasa
Sabon Shugaban ma'aiktan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce, aikin sa na farko da alhakin sa shi ne ya kai rahoto ga shugaban kasa kai tsaye, ba ga jama'a ba.     Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da ya yi magana a takaice ga manema labarai daga Fadar Shugaban Kasa, bayan sanarwar nadin nasa. Ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda zaben shi da akai bisa cancanta don gudanar da aiki a karkashin gwamnatin shugaban kasa Buhari.     An dai nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Najeriya ne tun bayan rasuwar tsohon shugaban ma'aikata Abba kyari wanda ya rasu bayan kamuwa da yayi da cutar corona.
Tarihin sabon shugaban ma’aikatan shugaban kasa,Farfesa Ibrahim Gambari

Tarihin sabon shugaban ma’aikatan shugaban kasa,Farfesa Ibrahim Gambari

Siyasa
Farfesa Ibrahim Gambari fitaccen malamin jami'a ne kuma ma'iakacin diflomasiyya da ya rike mukamai manya-manya a duniya da Afirka da kuma Najeriya.     An haifi Ibrahim Gambari a shekarar 1944, a Ilorin, jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.   Gambari ya yi sakandarensa a King's College da ke Lagos. Ya yi digirinsa na farko a London School of Economics inda ya kammala a 1968 kuma ya samu kwarewa a fannin harkokin kasashen waje.   Ya yi digirinsa na biyu da na uku a 1970 da 1974 a jami'ar Columbia University, New York d ake Amurka a fannin kimiyyar siyasa da harkokin kasashen waje.   Daga nan sai Farfesa Gambari ya koma jami'ar Ahmadu Bello University da ke Zaria a jihar Kaduna inda ya koyar daga 1977 zuwa 1980. &nbs...
Atiku,Saraki da Gwamnan Kwara sun taya sabon shugaban ma’aikatan Buhari, Ibrahim Gambari murna

Atiku,Saraki da Gwamnan Kwara sun taya sabon shugaban ma’aikatan Buhari, Ibrahim Gambari murna

Siyasa
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya taya sabon shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari murnar sabon mukamin da shugaba Buhari ya bashi.   A sakon daya fitar ta shafinshi na Twitter, Atiku Abubakar yayi fatan cewa Gambari yayi amfani da kwarewarsa wajan amfanar 'yan Najeriya. https://twitter.com/atiku/status/1260524695465721856?s=19   Shima dai tsohon gwamnan Kwarar kuma tsohon kakakin majalisar Dattijai,Bukola Saraki ya bayyana taya sabon shugaban ma'aikatan murna.   Saraki ya bayyana cewa,yana da yakinin Gambari zai yi nasara a aikin da aka bashi inda ya roki 'yan Najeriya su bashi hadin kai. https://twitter.com/bukolasaraki/status/1260523985638481921?...

Hotuna: Shugaban Ma’aikta farfesa Ibrahim Gambari ya isa fadar shugaban kasa

Uncategorized
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.   Sai dai kuma har yanzu Fadar Shugaban Kasar ba ta tabbatar da nadin Farfesa Gambari ba.   Mashawartan shugaban kasar a kan al’amuran yada labarai da ma jami’an ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya sun ki su ce uffan a kan lamarin. Sai dai sun bukaci manema labaran da suka tuntube su da su jira sanarwa a hukumance.