
Shugaba Buhari yasa sabon shugaban ma’aikatansa, Gambari ya soke abubuwan da Marigayi Abba Kyari yayi bada Umarninsa ba
Rahotanni daga fadar shugaban kasa na cewa akwai rade-radin shugaba Buhari ya sa sabon shugaban ma'aikatansa, Ibrahim Gambari ya soke duk wani abunda marigayi Abba kyari yayi bada Umarninsa ba.
Rahoton yace an gano wasu ayyuka da nade-nade har 150 da marigayi Abba Kyari yayi ba tare sa umarnin shugaban kasa ba kamar yanda, Guardian ta ruwaito.
Jaridar ta tuntubi me maganda yawun shugaba kasar, Femi Adesina akan wannan batu amma bai bata amsa ba saidai yace yana sakon data aika masa na waya.
Hakanan shima dayan me magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu bai bayar da amsa ba da aka mai tambaya kan lamarin.