fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: Farfesa Itse Sagay

Rashin tsaro yayi yawa, Ka bar kowane dan Najeriya ya sai makami dan kare kanshi>>Na kusa shugaba Buhari ya bashi shawara

Rashin tsaro yayi yawa, Ka bar kowane dan Najeriya ya sai makami dan kare kanshi>>Na kusa shugaba Buhari ya bashi shawara

Siyasa
Babban me baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara kan yaki da cin hanci, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa kamata yayi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa kowane dan Najeriya damar kare kansa daga matsalar tsaro.   Ya bayyana hakane a tattaunawar da yayi da Independent inda yace matsalar tsaron ta aki intaha ta yanda koda mutum a cikin gidansa bai tsiraba.   Ya bayyana cewa, ya rasa wane dalili ne ya sanya 'ya  Najeriya suka zama mutane masu tada fitina haka, yace yanzu tafiya a titi abune me matukar hadari. Yace lokacin suna matasa ba haka rayuwar take ba.   Yace shawarar da zai baiwa shugaba Buhari shine ya bar mutane,  Musamman wanda suke karkara su rika sayen makamai dan kare kansu kawai. “The country has become so dangerous. All sort...
Mun fa yi muku ta Arziki mun yi abinda kuke so, Idan ba ku daina Zanga-zanga ba zamu saka muku karfi>>Gargadin Gwamnati ga Masu zanga-zangar SARS

Mun fa yi muku ta Arziki mun yi abinda kuke so, Idan ba ku daina Zanga-zanga ba zamu saka muku karfi>>Gargadin Gwamnati ga Masu zanga-zangar SARS

Tsaro
Me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin yaki da rashawa da cin hanci, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa gwamnati ta ji kukan matasa ta kuma biya musu bukatunsu.   Yace dan haka ya kamata ace matasan sun hakira da zanga-zangar hakanan. Ya koka da cewa wasu bata gari sun fara shiga rigar zanga-zangar dan kawo rudani a kasar baki daya.   Da hakane yace idan ba'a daina zanga-zangar ba to gwamnati na iya amfani da karfin tuwo wajan hanata. Sagay yace an yiwa matasannan duk abinda suke so amma abu ya gagara karewa wanda hakan ke nuna cewa akwai wata manufa da ake son cimmawa akan wannan zanga-zanga ake fakewa da SARS.   Yace irin abinda ya faru kenan a Hongkong suma matasa aka musu duk abinda suke so amma suka ki hakura har kasar ta tsaya cak. Yace yaga ...
Malami na son dakatar da binciken da EFCC kewa wasu manyan ‘yan Siyasa>>Me baiwa shugaba Buhari shawara kan yaki da rashawa, Sagay yayi zargi

Malami na son dakatar da binciken da EFCC kewa wasu manyan ‘yan Siyasa>>Me baiwa shugaba Buhari shawara kan yaki da rashawa, Sagay yayi zargi

Siyasa, Uncategorized
Me baiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shawara kan yaki da rashawa, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa gyaran da ake son yiwa hukumar EFCC bai kamata ba.   Sagay yace ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari'a, Abubakar Malami ne kawai ke son yayi amfani da wannan dama wajan dakatar da binciken da akewa wasu manyan 'yan siyasa a kasarnan. Duk da Sagay bai kira sunan Malami ba amma ya bayyana sunan ofishinsa, yace gyaran bai kamata ba saboda ana son a mayar da EFCC din karkashin ofishin ministan shari'ar sannan kuma shine zai iya nada shugabanta.   Yace wanda suka kirkiro wannan gyara suna so ne su mayar da hukumar irin yanda take aiki kamin zuwan gwamnatin shugaba Buhari a shekarar 2015 inda ake kama karya da abinda aka ga dama.   ...
Arewa na shirya yiwa Kudu wayau dan ci gaba da rike shugabancin Najeriya a 2023>>Hadimin shugaba Buhari

Arewa na shirya yiwa Kudu wayau dan ci gaba da rike shugabancin Najeriya a 2023>>Hadimin shugaba Buhari

Siyasa
Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari dake bashi shawara akan yaki da cin hanci, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa akwai wani kulli da Arewa ke yi dan dan yankin ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.   Ya bayyana cewa masu kira da a zabi shugaban kasar da ya cancanta ai a kowane yanki akwai wanda ya cancanta. Hutudole ya samo muku wannan maganane ta Sagay daga jaridar Sunnews a hirar da ta yi da shi. Yace da ace masu kiran a zabi shugaban kasa saboda cancanta sun bari sai bayan yankin da bai yi shugabancin kasar ba ya kammala nashi shugabancin to da ya yadda dasu. Hutudole ya tattaro muku ya kara da cewa amma a yanzu kamata yayi ace wanda ya cancanta daga kudu.   Yace wannan salon wayaune dan kawai wani bangare ya ci gaba da rike mulkin kasarnan domin kowan...
Zamu zama jam’iyyar ci mu ci muddin ba’a kula ba, Abin kunyane dawowar Dogara APC>>Hadimin shugaba Buhari

Zamu zama jam’iyyar ci mu ci muddin ba’a kula ba, Abin kunyane dawowar Dogara APC>>Hadimin shugaba Buhari

Siyasa
Shugaban kwamitin dake baiwa shugaban kasa shawara kan yaki da cin Hanci, Farfesa Itse Sagay ya bayyana komawar tsohin kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara jam'iyyar APC a matsayin Abin kunya ga jam'iyyar.   A jiyane dai muka ji yanda Dogara ya bar PDP zuwa APC, inda gwamnan Yobe kuma shugaban kwamitin riko na APC, Mai Mala Buni ya mai jagora zuwa fadar shugaba Buhari inda suka gana da shugaban kasa. A martaninsa ga wannan Lamari, Sagay ya bayyana cewa gaskiya hakan bai kamata ta ba, ai da a APC Dogaran yake amma ya biyewa abokinsa, Saraki suka koma PDP, yace me yasa be ci gaba da zama acan PDP din ba, shine zai dawo APC, Yace watau shi a gunsa duk jam'iyyun daya ne kenan.   Sagay yace idan dai APC bata da banbanci da PDP to bai ga amfanin kwace mulki da su...
Kada ka halarci taron APC, Hadimin shugaban kasa Farfes Sagay ya baiwa Buhari shawara

Kada ka halarci taron APC, Hadimin shugaban kasa Farfes Sagay ya baiwa Buhari shawara

Siyasa
Hadimin shugaban kasa,Farfesa Itse Sagay ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kada ya halarci taron kwamitin gudanarwar APC da bangaren Victor Giadom ya shirya a yau.   Da yake hira da TheNation ya bayyana cewa da yaji wai shugaba Buhari na goyon bayan Victor Giadom ya kadu sosai, yace ta yaya ga mataimakin shugaban jam'iyya amma za'a ce mataimakin sakatarene zai zama shugaban jam'iyya? Yace Giadom ya dogara da wata dama da Kotu ta bashine a watan Maris wadda ta yi aiki ne a kwanaki 14 kawai, kumama shi kadai ya halarci kotun.   Yace kwatsam sai ga shi yanzu ya bayyana yana cewa wai kuma kotu ta kara tsawaita wannan dama a watan Yuni. Yace gaskiya abin akwai ban mamaki.   Yace yana baiwa shugaba Buhari shawarar kada ya halarci wannan taro da ...
Idan Buhari bai yi magana akan rikicin APC ba to PDP zata karbe jihar Edo>>Hadimin shugaban kan Yaki da Rashawa

Idan Buhari bai yi magana akan rikicin APC ba to PDP zata karbe jihar Edo>>Hadimin shugaban kan Yaki da Rashawa

Siyasa
Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari dake bashi shawara kan yaki da rashawa da cin hanci, Farfesa, Itse Sagay ya bayyana cewa shugaban a wannan karin ya kamata yayi magana kan rikicin dake faruwa a jam'iyyar.   Yace shirun na shugaban kasar yayi yawa, dan kuwa idan bai saka baki ba, jam'iyyar naji tana gani zasu rasa jihar Edo a hannun 'yan adawa na PDP. Ya bayyana hakane a hirar da yayi da manema labarai na jaridar Independent inda yace lamarin yayi muni inda har ta kai ga cewa mataimakin sakataren jam'iyyar na fitowa ya ce shine shugaba to ya kamata a saka baki.   Yayi zargin cewa an bari 'yan leken Asiri sun shiga jam'iyyar shiyasa suke ganin irin wannan lamari.
Za’a iya kama ‘yan majalisar tarayyar da suka ki yadda a musu gwajin Coronavirus/COVID-19

Za’a iya kama ‘yan majalisar tarayyar da suka ki yadda a musu gwajin Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Farfesa Itse Sagay wanda shine shugaban kwamitin dake baiwa shugaban kasa,Muhammadu Buhari shawara kan yaki da rashawa da cin hanci yace duk wanda yaki yadda a mai gwajin cutar Coronavirus/COVID-19 zai iya fuskantar fushin hukuma.   Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da jaridar Daily Independent inda yace ya ji rahoton dake cewa wasu 'yan majalisar tarayya da suka dawo daga kasashen waje sun ki yadda a gwadasu.   Yace duk da me magana da yawun majalisar ya karyata wannan rahoto amma indai ya zama gaske to akwai rashin sanin ya kamata a ciki. Kuma asani duk wanda yaki yadda a gwadashi zai iya fuskantar fushin hukuma, duk kuwa girman matsayin da yake rike dashi.   Farfesa Sagay da yake magana akan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na dakile yaduwar cutar...