
Hotuna: Farin dangon da ka iya cinye mutum dubu 35 a lokaci guda sun kacalcala gonaki a India
Dimbin farin-dango da adadinsu ya haura miliyan 200 na lalata albarkatun gona a sassan Yammaci da kuma Tsakiyar kasar India, lamarin da ya sa hukumomi suka zage damtse wajen magance iftila’in, mafi muni a kasar cikin shekaru 30 da suka gabata.
Hukumomin na India sun tura jirage marasa matuki da tantan da kuma kananan motoci domin gano wadannan farin-dangon tare da feshe su da magungunan kashe kwari.
Sai dai tuni farin suka lalata kusan kadada dubu 50 a gonaki, yayinda gwamnatin India ta ce, ana samun tawaga-tawaga na farin daga takwas zuwa 10 a wasu yankuna na Rajasthan da Madhya Pradesh.
Barnar da farin suka yi na zuwa ne a daid...