fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Fasaha

Hotuna:Dan Asalin Jihar Sokoto ya kera Transformer wutar lantarki

Hotuna:Dan Asalin Jihar Sokoto ya kera Transformer wutar lantarki

Uncategorized
Dan Asalin jihar Sokoto, Anas Aliyu Boyi, ya kera Transformer ta wutar Lantarki inda ya gabatar da ita a wajan baje kolin fasaha da aka gudanar a jihar.   Me baiwa gwamnan shawara akan sana'o'in dogaro da kai, Nafiu Bello Basakkwacene yayi shiryawa wannan taro, kamar yanda shafin gwamnatin jihar ya tabbatar. https://twitter.com/SokotoGovtHouse/status/1330210083435929605?s=19 Today, Anas Aliyu Boyi who hails from Sokoto-South Tudun Wada LGA constructed a Modern day ‘TRANSFORMER’ which he presented at the Global Entrepreneurship week summit organized by the Special Adviser @BelloBasakkwace on Skill Acquisition and powered by H.E @GovSokoto @AWTambuwal
Hotunan yanda wani matashi a Bauchi ya mayar da Keke Napep dinsa me amfani da hasken Rana, ba ruwansa da sayen Fetur

Hotunan yanda wani matashi a Bauchi ya mayar da Keke Napep dinsa me amfani da hasken Rana, ba ruwansa da sayen Fetur

Uncategorized
Wannan wani matashi ne daga jihar Bauchi wanda ya mayar da Keke Napep dinsa tana aiki da hasken rana.   Yanzu bau ruwansa da sayen Man Fetur. Hotuna  nashi sun dauki hankula bayan da aka sakasu a shafukan sada zumunta. https://twitter.com/OvieSheikh/status/1326249430106910727?s=19 https://twitter.com/OvieSheikh/status/1326249430106910727?s=19
FASAHA: Wani Matashi Dan Jihar Katsina Ya Kirkiro Na’urar Bayyana Tashin Gobara Nan Take

FASAHA: Wani Matashi Dan Jihar Katsina Ya Kirkiro Na’urar Bayyana Tashin Gobara Nan Take

Uncategorized
Malam Umar Liman Faskari, ya kirkiro wata na'ura wadda take bayyana faruwar gobara nan take kuma za ta fara kara har ta ankarar da mai itah cikin kankanin lokaci.   Malam Umar Liman Faskari ya ce, ya dau lokaci yana hada na'urar har Allah Ya ba shi damar kammala ta.   Ana saka na'urar a daki da falo da kuma da tsakar gida, yadda da wata wuta ta tashi kowa zai ankara da karar da zata fara har sai an kawo dauki tayi shiru.   Ya kuma bayyana cewa, duk da karancin kudin da yake fuskanta akwai wasu kirkire-kirkiren da zai yi wadanda za su kawo ci gaba sosai wajen more rayuwa da inganta ta.   Kuma fatan mu shine gwamnati za ta rika taimakawa irin wadannan masu basirar, ko ba don komai ba, don rage zaman banza.