fbpx
Sunday, May 22
Shadow

Tag: Fashi da Makami

‘Yansanda sun kama dan tsohon Ministan Najeriya da ya je fashi da makami

‘Yansanda sun kama dan tsohon Ministan Najeriya da ya je fashi da makami

Siyasa
'Yansandan Najeeiya sun kama dan tsohon Ministan Najeriya da zargin fashi da makami wanda yanzu haka yana can a tsare.   Dan Ministan ya kaiwa wani wajan canjin kudi harine a Abuja. Mun tattaro muku daga TheNation cewa dan Tsohon Ministan da ya fito daga jihar Benue na can ana tsare dashi ana bincike.   Wata Majiya ta shaida cewa dan Tsohon Ministan ya je wajan 'yancanjin da Bindiga irin kirar gida da niyyar yin fashin amma sai 'yan sakai suka lallaba suka kamashi suka mai dukan kawo wuka.   Yaje satar ne da motar mabaifinsa, itama fusatattu sun mata kaca-kaca. Daga baya an mikashi hannun jami'an tsaro.   Dan tsohon Ministan dai yana aiki da wata ma'aikatar gwamnatin tarayya ne. Amma ya saba da samun makudan kudi a sama shiyasa yaje fashin...
Yanda Wani gawurtaccen dan fashi dake Daure a gidan yari ya shirya fashi da makami a banki, Cikin yaransa hadda tsaffin sojojin Najeriya

Yanda Wani gawurtaccen dan fashi dake Daure a gidan yari ya shirya fashi da makami a banki, Cikin yaransa hadda tsaffin sojojin Najeriya

Tsaro
'Yan fashin da aka kama da zargin hannu a fashin bankinda aka yi a Ebonyi wanda dalilinsa aka kashe 'yansanda 2 sun bayyana cewa wanda ya shirya fashin na daure a gidan yari.   Sun bayyana cewa ogansu wanda ya shirya fashin sunansa Clement Abanara dake daure a gidan yarin Ikoyi na jihar Legas. Fashin ya farune a watan Yuli ds ya gabata. Cikin 'yan fashin akwai korarrun sojoji, Emeka Ariston da Ayeni Samuel, sai kuma dan uwan shugaban 'yanfashin me suna, Alfred Robinson, da Sunday Solemu, Abuchi Alfred, Emeka Ilo, da Ekene Igbanifore.   An kwace bindigun AK47 6 a hannunsu da tulin makamai da kotoci 2 na sata da kuma wasu kayan tsubbu.   Da yake bayar ds Labari, Ayeni yace an hadashi da Abanara dake gidan yari bayan rasa aikinsa na soja inda kuma aka c...
Hotuna an kama mace me ciki wata 9 cikin ‘yan fashi da Makami

Hotuna an kama mace me ciki wata 9 cikin ‘yan fashi da Makami

Siyasa
Jami'an tsaro a jihar Edo sun kama wasu da ake zargi da fashi da makami su 3, wani abin mamaki shine akwai wata mace me dauke da ciki wata 9 a cikinsu.   Kakakin 'yansandan jihar, Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai inda yace sunayen wadanda aka kama din, Jumoke Akanbieme, Osagiede Izevbokun da Godfrey Okonide.   Yace suna amfani da matar me ciki ne inda take tsayawa a bakin titi da nufin neman taimako,  da mutum ya tsaya sai su masa fashi. Yace dubunsu ta cika ne bayan da suka kwacewa wani mutum mota da niyyar yanka ta a sayar da guntu-guntunta.   Ita matar me ciki da aka kama tace saurayinta ya saka ta cikin wannan mummunar sana'a.
Kwaya muke basu muna sace musu kudi>>Wani Dan Fashi da aka kama

Kwaya muke basu muna sace musu kudi>>Wani Dan Fashi da aka kama

Uncategorized
Wani dan fashi da jami'an tsaro a jihar Naija Suka kama ya bayyana cewa Kwaya yake baiwa mutanen da yakewa sata.   An kama Abdullahi Mai Kudi dan kimanin shekaru 27 daya fito daga jihar Katsina tare da abokin masha'arsa, Abdullahi Rabiu da ya fito daga jihar Kano bisa zargin satar kudi, Miliyan 6. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Abiodun  ya tabbatar da kamen inda yace an kwato Miliyan 3.8 daga hannun wanda ake zargi. Mai Kudi ya amsa laifinsa.