
Mutane 2 sun mutu, an harbi dan sanda a fashin hanyar Kogi
Lamarin ya farune da misalin karfe 6 na yammacin jiya, Lahadi a daidai Osara, tsakanin Itakpa da Kabba inda 'yan fashi suka bude wuta.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan Fashin sun kashe mutum 2 tare kuma da harbin wasu ciki hadda dan sanda.
Wanda suka mutu din 'yan asalin Kogi ne dake zaune a jihar Katsina, kuma sun dawo daga ganin gidane yayin da lamarin ya faru.
Wata mata data tsallake harin ta shaidawa Punch cewa, harin ya saka fargaba azukatan mutane kuma da dama sun shiga halin kaka nikayi inda aka tara motoci da yawa akan hanya.
Saidai 'yansandan jihar sunce basu da masaniya akan wannan hari.