
2023: Inyamurai basu da yawan da zasu samar da shugaban kasa>>Fasto Tunde Bakare
Fasto Tunde Bakare, Shugaban Cocin Citadel Global Community dake Legas ya bayyana cewa inyamurai basu da yawan da zasu samar da shugaban kasa a Najeriya.
Ya bayyana hakane a wata hira da me mujallar Ovation Magazine, Watau Dele Momodu inda yace ko kadan ba wai baya shiri da iyamurai bane yace yana sonsu kuma yana musu fatan Alheri.
Yace amma jam'iyyar APHA ba zata iya samar da shugaban kasa ba, yace dolene sai Inyamurai sun shiga siyasar kasa an dama dasu kuma sun hada kai da kudu da arewa saboda ita Dimokradiyyar tana amfani da yawan jama'a ne, yace kada su koma gefe suna kukan cewa ana nuna musu wariya.
“The Igbos are my brothers and sisters, God bless them, I love them and I care about them. They should also come to mainstream politics because APGA as a ...