fbpx
Thursday, May 26
Shadow

Tag: Femi Falana

Abin kunyane ace Dangote ya gina matatar mai amma gwamnati ta kasa ginawa>>Femi Falana

Abin kunyane ace Dangote ya gina matatar mai amma gwamnati ta kasa ginawa>>Femi Falana

Siyasa, Uncategorized
Banban lauya, Femi Falana, SAN, ya bayyana cewa abin kunyane yanda Gwamnatin tarayya ta kasa gina matatar mai me kyau, amma a matsayin dan kasuwa, Dangote ya iya gina matatar man.   Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Vanguardlivetv, inda yake martani qkan maganar karin kudin man da PPPRA ta yi wanda daga baya gwamnati ta musantashi.   Ya bayyana cewa PPPRA ta tashi kawai ta kara kudin man fetur wanda Minista ne kadai ke da alhakin hakan. Yace amma abin mamaki shine babu wanda aka hukunta akan lamarin.   Yace duk shekara sai an ware makudan kudade dan gyaran matatun man Najeriya amma sai a ci gaba da shigo da man daga kasashen waje. It is a shame that an individual like Dangote can build a refinery to refine 600 barrels of oil per day and...
A lokacin Mulkin Jonathan, Buhari yace yayi Murabus amma ba’a kamashi ba, dan haka a Saki Salihu Tanko Yakasai>>Femi Falana

A lokacin Mulkin Jonathan, Buhari yace yayi Murabus amma ba’a kamashi ba, dan haka a Saki Salihu Tanko Yakasai>>Femi Falana

Siyasa
Babban Lauya kuma me ikirarin kare hakkin bil'adama, Femi Falana ya bayyana cewa a lokacin Mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan Shugaba Buhari yayi kura da cewa shugaban yayi Murabus amma ba'a kamashi ba.   Yace Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Ministan yada labarai da Al'adu na yanzu, Alhaji Lai Muhammad na daga cikin wanda suka yi irin wancan kiraye-kiraye.   Yace akwai kuma 'yan Majalisa da manyan 'yaj APC da suka yi kiran shugaba Buhari yayi Murabus amma duk ba'a kamasu ba sai Hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai?   Yace dan haka suna Kira da cewa a gaggauta sakinsa daga daurin da ake masa ba tare da wani sharadiba.   “On Friday, February 27, 2021, Mr. Salisu Tanko-Yankassai, the Special Adviser on Media to Gover...
An maka babban Lauya Femi Falana a Kotun Duniya ta ICC

An maka babban Lauya Femi Falana a Kotun Duniya ta ICC

Siyasa
Wata kungiya ta MNBI ta bayyana cewa ta maka babban lauyannan na Najeriya, Femi Falana a kotun Duniya ta ICC bisa hannu da take zarginsa dashi a zanga-zangar SARS.   Hakan na zuwa ne bayan da Falana ke kokarin ganin ya gurfanar da shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai a gaban kotun.   Kungiyar ta bayyana cewa zanga-zangar da Falana ya zuzuta ta kai ga sanadiyyar Asarar rayuka sannan ta zargi lauyan da kuma nuna kiyayya ga jami'an tsaron Najeriya musamman sojoji.  
Ni ban yadda kudin shigar Najeriya sun ragu da kaso 65 ba, karyace kawai gwamnati take dan ta kare karin kudin mai dana wutar lantarki da ta yi>>Femi Falana

Ni ban yadda kudin shigar Najeriya sun ragu da kaso 65 ba, karyace kawai gwamnati take dan ta kare karin kudin mai dana wutar lantarki da ta yi>>Femi Falana

Siyasa
Babbau lauya kuma me rajin kare hakkin bil'adama ya karyata Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad da ta yi ikirarin cewa kudin shigar Najeriya sun ragu da kaso 65 cikin 100.   Zainab ta bayyana cewa dalilin hakane ma yasa gwamnati dole ta zare hannun ta daga tallafin mai sannan kuma aka kara kudin wutar lantarki a wata hira da Channelstv ta yi da ita. Saidai Femi Falana a karkashin kungiyar da yake jagoranta, ta kokarin ganin an tsallake matsalolin da cutar Coronavirus/COVID-19 ta zo dasu(ASCAB) ya bayyana cewa wannan ikirarin na ministar karyace kawai.   Yace za'a iya fahimtar cewa Ministar karya take idan aka lura da kudin da gwamnatocin tarayya, Jihohi da kananan hukumomi suka raba tsakaninsu a watanni 6 na farkon wannan shekarar ya fi na shekarar data gabata...
Bayan daukaka karan wanda aka yankewa hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi(SAW), Femi Falana ya kai Gwamnatin Tarayya data Kano kara wajan kungiyar kare hakkin bil’adama ta Africa

Bayan daukaka karan wanda aka yankewa hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi(SAW), Femi Falana ya kai Gwamnatin Tarayya data Kano kara wajan kungiyar kare hakkin bil’adama ta Africa

Uncategorized
Babban lauya kuma me rajin kare hakkin bil'adama,  Femi Falana bayan daukaka karar hukuncin kisa da aka yankewa wanda yawa Annabi,(SAW) batanci a Kano, ya kuma kai karar Gwamnatin jihar Kano data Najeriya game da wannan lamari gurin kungiyar kare hakkin bil'adama ta Africa dake Banjul, Gambia.   Falana a sakon da ya aika ya nemi kungiyar da cewa ta shiga wannan magana saboda an takewa Yahaya Sharif hakkinsa inda ake neman zartar masa da hukuncin kisa. Falana yace duk da an daukaka kara amma maganar gaskiya babu tabbacin za'a wa Sharif Adalci a wannan hukunci.   Kungiyar Tuni ta amsa cewa ta samu sakon Falana kuma zata fara aiki akai, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.
Karya ake min ban karbi Miliyan 28 daga Hannun Magu ba>>Lauya, Femi Falana

Karya ake min ban karbi Miliyan 28 daga Hannun Magu ba>>Lauya, Femi Falana

Siyasa
Babban lauya kuma me kare hakkin bil'adama,  Femi Falana ya bayyana cewa, baisan da maganar Miliyan 28 da ake dangantashi da ita ba tsakaninshi da Magu.   Falana yayi maganane ta bakin Lauyansa, Adeyinka Olumide Fusika(SAN) wanda ya ce yana kira ga Jaridar data wallafa wanan labari ta cireshi kuma ta bashi hakuri. Yace ya baiwa Jaridar awanni 48 ta cire labarin kuma wannan bukatace cikin ruwan sanyi wanda idan ba ta yi ba zai dauki matakin shari'a.   Rahoton dai ya bayyana cewa kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ne ya kawo bayanai kan rahoton da kwamitin dake binciken magu ya hada ya mikawa shugaba Buhari.
Maganar Magu Abin Kunyane ga shirin yaki da cin hanci na gwamnatin Buhari>>Femi Falana

Maganar Magu Abin Kunyane ga shirin yaki da cin hanci na gwamnatin Buhari>>Femi Falana

Siyasa
Shahararren lauya me ikirarin kare hakkin bil'adama,  Femi Falana ya bayyana cewa abin kunyane lamarin zarge-zargen da akewa Ibrahim Magu ga shirin yaki da cin hanci na gwamnatin shugaba Buhari.   Yace ya kamata ace shugaban EFCC ya zamana cewa ta bangaren Almundahana dai kada a sameshi da laifi. Yace idan aka yi duba a baya za'a ga cewa yawancin shuwagabannin EFCC kodai a saukesune ko kuma a zargesu da Almundahana.   Yace amma maganar Magu tasha banban da sauran saboda shi gwamnatin data nadashine take bincikenshi.   Yace amma yasan za'a baiwa Magu damar bayani kan zarge-zargen da ake masa kuma idan yayi nasarar wake kanshi to shikenan idan kuma ya kasa sai a masa hukunci.   Falana ya bayyana hakane yayin da yake magana a wani shiri na gi...
Sanata Shehu Sani, Gali Umar Na Abba, Femi Falana da wasu sauran manyan ‘yan Najeriya na shirin bude sabuwar jam’iyya

Sanata Shehu Sani, Gali Umar Na Abba, Femi Falana da wasu sauran manyan ‘yan Najeriya na shirin bude sabuwar jam’iyya

Uncategorized
Wasu fitattun 'yan Najeriya sun hada kai inda suka yi shirin fito da wata sabuwar jam'iyya da a cewarsu zata fitar da kasarnan daga matsalar da take ciki.   A yanzu dai sun sakawa kungiyar tasu sunan National Consultative Front kuma sun bayyana cewa bayan tattaunawa da kuma tuntuba da masu ruwa da tsaki, sun yanke shawarar buxe sabuwar jam'iyyar.   Daga cikin membobin wannan kungiya 30 akwai Femi Fala(SAN), Sanata Shehu Sani, Tsohon kakakin majalisar wakilai, Ghali Umar Na'abba, Alhaji Shattima Yarima,  Obigeli Ezekwesili dadai sauransu.   Sun kara da cewa sun damu da matsalar hare-haren ta'addanci dake faruwa a kasarnan da da suka hada da sace mutane dan neman kudin fansa.