fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Femi Fani Kayode

Abokiyata ce kawai, ba aurenta zan yi ba>>Tsohon Minista, FFK yayi karin haske kan labarin aurensa da tauraruwar fina-finan Hausa,Halima

Abokiyata ce kawai, ba aurenta zan yi ba>>Tsohon Minista, FFK yayi karin haske kan labarin aurensa da tauraruwar fina-finan Hausa,Halima

Nishaɗi
A baya mun samu labari daga Kemi Olunloyo cewa Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode zai auri tauraruwar fina-finan Hausa, Halima Yusuf.   Kemi tace Femi da Halima sun shafe kusan shekara daya tare kuma a yanzu yana shirin aurenta a matsayin matarsa ta 5.   Saidai a martaninsa, Femi Fani Kayode ya karyata wannan ikirari inda yace shi da Halima abokaine kawai, babu maganar aure a tsakaninsu.   Yace ita da sauran wasu abokansa suna matukar kwantar masa da hankali inda yace shiyasa yake ganin kimarta. Ya kara da cewa masu maganar cewa zai aureta su daina, ba gaskiya bane.
Matar Tsohon Minista, Femi Fani Kayode ta yi magana bayan Mutuwar Aurensu

Matar Tsohon Minista, Femi Fani Kayode ta yi magana bayan Mutuwar Aurensu

Uncategorized
Matar tsohon ministan sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode, Precious Chikwendu ta yi magana a karin farko tun bayan rabuwarsu da mijin nata.   Tsohuwar sarauniyar kyan Najeriya ta saka a shafinta na Instagram cewa, Allahbya kubutar da ita. Bata dai yi cikakken bayani ba amma ta saka wani sashe ne ne Baibul dake nuna Allah ya kubutar da mutum daga wata wahala da ya shiga. Saidai a gefe daya dangin mijin nata sun bayyanawa Premium times cewa sun rabune saboda matar tana yawan fita ba tare da izinin mijin nata ba wanda abin ya isheshi kuma tana da wani ciwo da tun lokacin auren su ake faman neman magani amma abu ya ci tura.   Ta bangaren dangin matar kuwa, Wani kawunta ya bayyanawa majiyar tamu cewa tabbas sun rabu kusa  wata 1 daya gabata amma maganar gaskiya ...
Tsohon Minista, Femi Fani Kayode ya saki matarsa

Tsohon Minista, Femi Fani Kayode ya saki matarsa

Uncategorized
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya rabu da matarsa, Precious Chukwendu.   Saidai ya nemi me shafin Stella Dimokokurs ta biyashi diyyar karyar data masa na Biliyan 2 da kuma neman afuwarsa kan karyar da yace ta masa na cewa dalilin cin zarafine ya rabu da matar tasa. Yace wannan abu da me shafin ta fada yasa mutanen da suka sanshi cikin damuwa wanda hakan ya bata masa suna.
Femi Fani Kayode ya bukaci Daily Trust ta biyashi Biliyan 6 saboda zargin bata suna

Femi Fani Kayode ya bukaci Daily Trust ta biyashi Biliyan 6 saboda zargin bata suna

Siyasa
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ya bukaci jaridar Daily Trust data biyashi diyyar Biliyan 6 saboda zargin bata suna.   Daily a wata caccaka da wani Iliyasu Gadu ya rubuta kuma ta wallafa wanda lamarin ya dauki hankula sosai ta bayyana FFK a matsayin dan kwaya wanda har kasar Ghana ya je neman magani amma har yanzu be warke ba. Da yake magana akan wannan rubutu ta bakin  Lauyansa, Adeola Adesipe, FFK ya bayyana cewa wannan abu ya sa sunansa ya baci dan haka ya baiwa Daily Trust kwanaki 14 ta cire labarin sannan ta bashi hakuri ta kuma buga a sauran wasu gidajen Jaridu 2 da kuma biyanshi Biliyan 6 in ba haka ba zai garzaya kotu.
Dama Dan Can Dan Kwaya ne>>Dailytrust tawa Fani Kayode zagin kare dangi

Dama Dan Can Dan Kwaya ne>>Dailytrust tawa Fani Kayode zagin kare dangi

Siyasa, Uncategorized
Bayan cin zarafin da yawa wakilin jaridar Daily Trust, Eyo Charles a jihar Cross-Rivers, Tsohon Ministan Sufuri, Femi Fani Kayode da alama ya debo da zafi. A baya yace ba zai taba bada hakuri ba amma da Allah wadai ta yi yawa akan abin da yawa dan jaridar ya fito ya bada hakuri in yace yasan yayi abin kunya.   Saidai ga dukkan alamu JAridar ta Daily Trust bata yafe abin da yayi ba, A wata Wallafa da ta yi me matukar daukar hankali,Daily Trust ta bayyana FFK a matsayin dan kwaya, tace da yaje kasashen Turai karatu ya yi ta taammuli da miyagun gwayoyi ta yanda har abin ya zamar masa jiki.   Tace saida yayi ta neman magani hadda na gargajiya, kai harkasar Ghana ya je amma ga dukkan alamu har yanzu be warke ba. Ta ce ko da a jam'iyyarsa ta PDP babu me daukarsa da muhimman...
Babu tambayar shirme a aikin jarida>>Fadar shugaban kasa ta yi magana akan zagin da Fani Kayode yawa dan Jarida

Babu tambayar shirme a aikin jarida>>Fadar shugaban kasa ta yi magana akan zagin da Fani Kayode yawa dan Jarida

Siyasa
A karin farko fadar shugaban kasa ta yi magana akan zagin da tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode yawa dan jaridar Dailytrust.   Kayode yawa Eyo Charles zaginne a yayin da ya mai tambayar shin wanene ke daukar nauyin ran gadin da yake?. Tambayar tasa Kayode yawa dan jaridar tatas inda kuma hakan ya jawo cece kuce sosai. Amma daga baya ya bayar da Hakuri   Da yake mayar da martani kan zagin da Kayode yawa dan jaridar, Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewq babu tambayar bamza a aikin jarida saidai amsar banza. Hutudole ya samo muku daga shafin Garba Shehu na Twitter yana cewa, tsohon Ministan ya koyi darasi. https://twitter.com/GarShehu/status/1300082575252299779?s=19 Saidai Garba be kira sunan Ministan ba amma da y...
Na yi abin kunya, ka yafe min>>Fani Kayode ya roki Dan Jaridar da yawa kaca-kaca

Na yi abin kunya, ka yafe min>>Fani Kayode ya roki Dan Jaridar da yawa kaca-kaca

Siyasa
Tsohob Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode a karshe dai ya saduda kan cin zarafin da yawa dan jaridar Dailytrust.   Kayode ya zazzagi dan jaridar, Eyo Charles bayan da ya mai tambayar ko wanene ke daukar nauyin ran gadin da yake a jihohi?. Kayode ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Akwa-Ibom inda yace yayi abin kunya da ya saka iyalanshi abokai da iyayen gidanshi cikin damuwa.   Yace a yanzu yayi nadama bai kamata yawa dan jaridar abinda ya masa ba kuma yana fatan zai yafe masa.
Femi Fani Kayode ya bada hakuri kan zagin da yawa Dan jaridar Daily Trust

Femi Fani Kayode ya bada hakuri kan zagin da yawa Dan jaridar Daily Trust

Siyasa
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode bayan cin zarafin da yawa wakilin jaridar Daily Trust a jihar Cross-River da hakan ya jawo cece-kuce ya bada hakuri.   Kayode ya zagi dan jaridar bayan da ya tambayeshi wake daukar nauyin rangadin ganin ganin ayyukan da yake a jihohi kusan 6. Hutudole ya ruwaito muku kungiyar 'yan Jaridu ta Duniya, data Najeriya da Daily Trust da SERAP duk sun yi Allah wadai da abinda Femi yayi inda 'yan Najeriya da dama suma suka rika caccakar sa a shafukan sada zumunta. A baya yace yana nan kan bakansa saidai da safiyar yau ya bayyana cewa bayan shawara da masu bashi shawara ya janye zagin da yawa dan jaridar. Hutudole ya fahimci Kayode yace yana da abokai 'yan jarida kuma yana girmama aikin dan haka ba zai yi abinda zai bata aikin...
Bidiyo: Kungiyar ‘yan Jarida ta Duniya, Kungiyar ‘yan Jarida ta Najeriya da Dailytrust sun yi Allah wadai da cin Zarafin da Femi Fani Kayode yawa dan jarida

Bidiyo: Kungiyar ‘yan Jarida ta Duniya, Kungiyar ‘yan Jarida ta Najeriya da Dailytrust sun yi Allah wadai da cin Zarafin da Femi Fani Kayode yawa dan jarida

Uncategorized
Lamarin ya farune a jihar Cross-River inda tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ke tattaunawa da 'yan jarida kan ran gadin ayyuka da yake.   Wakilin Daily Trust,  Eyo Charles ya tambayi tsohon ministan cewa yace ya je jihohi 6 inda yake duba ayyukan da ake shin wake daukar Nauyinsa. Hutudole ya ruwaito muku cewa nan fa Ministan ya hasala ya fara zagin dan jaridar, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba inda yake tambayar dan jaridar shin yasan ko shi wanene? Shi fa tsohon Minista ne dan haka kada ya sake masa irin wannan tambayar, ya zargi dan jaridar da cewa wani ne ya aikeshi ya masa wannan tambaya dan ya kunyatashi.   Saidai a Bidiyon da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta an ga dan jaridar yana baiwa Kayode Hakuri. Hutudole ya fahimci Baya...
Dalilin da yasa nake goyon bayan A’isha Buhari>>Fami Kayode

Dalilin da yasa nake goyon bayan A’isha Buhari>>Fami Kayode

Uncategorized
Tsohon Ministan Sufurin jiragen Sama, Femi Fani Kayode ya bayyana cewa dalilin da yasa yake goyon bayan matar shugaban kasa shine itace hasken fadar shugaban kasar.   Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda ya kewa A'isha Buhari mutnar dawowa daga Dubai inda aka duba lafiyar ta. Hutudole ya fahimci cewa amma Kayode yace masu tunanin wannan yabo da yawa A'isha Buhari alamace ta cewa yana son komawa APC suna mafarki ne. Ya kara da cewa dama can shi yana goyon bayan matar shugaban kasar duk da yake cewa yana adawa da salon mulkin Mijinta. Hutudole ya tattaro cewa Kayode yace masu cewa kuma saboda ana adawa da mulkin gwamnatin mijinta kada a tayata murnar dawowa Najeriya su kuma basu kyauta ba.