
Sarkin Shinkafi ya baiwa Tsohon Ministan jiragen Sama, Fani Kayode Sarautar “Sadaukin Shinkafi”
Sarkin Shinkafi a jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Makwashe ya baiwa tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani Kayode Sarautar Sadaukin Shinkafi.
Hakan na kunshene cikin wata sanarwa da Sarkin ya fitar inda yace an baiwa tsohon Ministan wannan mukami ne saboda irin taimakawa ci gaban masarautar Shinkafi da yake.
Ya kara da yin kira ga tsohon Ministan da ya ci gaba da aikin taimakawa ci gabam masarautar.
Shima a nashi sakon, Fani Kayode da yake magana a Gusau, Babban Birnin jihar Zamfara ya bayyana godiya da wannan nadin sarauta. Yace zai yi kokarin ci gaba da ganin ya dabbaka kyakkyawar alakar dake tsakaninshi da Arewa.
Ya kuma yabawa gwamna Matawalle bisa ayyukan raya kasa irin su ginawa Fulani Ruga da ginin Filin jirgin sama da kuma ko...