
Hotuna:Attajirin Najeriya, Femi Otedola ya saiwa ‘ya’yansa mata 3 motocin Alfarma na Ferrari
Attajirin Najeriya wanda ya shahara wajan kasuwancin Man Fetur, Femi Otedola ya saiwa 'ya'yansa 3 mata motocin Alfarma na Ferrari.
Daya daga cikin 'ya'yan nasa, DJ Cuppy ce ta bayyana haka ta shafinta na sada zumunta. Sautan 'yan uwan nata sune Temi, Tolani Otedola.
Kowace motar Ferrari ana sayar da ita akan akalla Dala Dubu Dari 2 wanda sama da kwatankwacin Naira amiliyan 77 ne.