
A gobe Talata ne za’a fara aikin matasa 774,000 na gwamnatin tarayya>>Festus Keyamo
Bayan daga fara aikin a lokuta da dama a baya, a karshe dai gwamnatin tarayya ta sanar da cewa a gobe Talata ne idan Allah ya kai mu za'a fara aikin na matasa 774,000 a fadin Najeriya.
Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo ya sanar da cewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amince da a fara aikin.
“President Muhammadu Buhari has approved the take off of the Special Public Works Programme (engaging 774,000 unemployed itinerant Nigerians) to begin nationwide on Tuesday, January 5th, 2021. All NDE state structures are already in top gear for the take-off ceremonies.”