
FIFA ta dakatar da shugaban ƙwallo na Haiti har abada bayan bincike ya gano yana lalata da yara kanana:
FIFA ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafa ta Haiti Yves Jean-Bart har na tsawon rayuwarsa tare da cin sa tarar sama da dala miliyan a ranar Juma’a.
Jean-Bart mai shekaru 73 FIFA ta same shi da laifin cin zarafin mukaminsa da kuma yin lalata da cin zarafin 'yan wasa mata daban-daban, ciki har da kananan yara, kwamitin da'a mai zaman kansa na hukumar kwallon kafa ta duniya ya yanke hukunci.